Dandalin Kannywood: BMB ya caccaki manyan masana’antar shirya fina-finan Hausa

Dandalin Kannywood: BMB ya caccaki manyan masana’antar shirya fina-finan Hausa

Fitaccen jarumin nan dandalin shirya finafinan Hausa kuma mazunin garin Jos, Bello Mohammed Bello wanda aka fi sani da General BMB ya caccaki manyan yan Kannywood akan wariya da suka nuna wa abokan sana’arsu na Jos.

Jarumin na martani ne ga rashin gayyatar yan Jos da ba a yi ba a yayin bikin kaddamar da sabuwar manhajar saida finafinan Hausa akan yanar gizo mai suna Northflix.

An dai gudanar da taron ne otel din Bristol da ke garin Kano, taron ya samu hallartan masu shirya fina-finai da manyan jarumai da wasu masu ruwa da tsaki a harkar fim.

Sai dai hakan bai yiwa BMB dadi ba domin ba a gayyaci yan Jos ba, inda ya nemi sanin ko an yakice su daga Kannywood ne.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa aka haramta yin tashe a Kano

Ga yadda ya wallafa a shafinsa na Instagram: “Ko dai an cire Jos ne daga Kannywood! Abin cigaba yazo na Northflix an qi gayyatar mu, anyi meeting farko na loan, an gayyace ni, ni kadai nazo na har kano na dauki nauyin kaina daga transportation har hotel, amma daga baya an yi committee babu Bello babu gayyatar Bello.

"Kuma tare mukayi yaqin second term din @govumarganduje da zai bada loan din. Anci moriyar ganga ne an yar da kwauren koko yaya?

"Ba'ayimin adalci ba, amma Allah ya buda mana ta hanyar da tafi imganci a gare ni, hanyar Allah na da yawa. MUNAFUNCI DAI UBANGIJIN SHI YAKE CI KUMA MU NA NAN A A.P.C din bana chanja aqida don kaifi daya nake.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng