An kashe sojan Najeriya a kasar Mali

An kashe sojan Najeriya a kasar Mali

Rundunar tsaron majalisar dinkin duniya dake aikin tabbatar da zaman lafiya a kasar Mali ta sanar da kisan wani sojan Najeriya a ranar Lahadi sakamakon wani harin 'yan bindiga.

Stephane Dujarric, kakakin sakataren majalisar dinkin duniya (MDD), ta ce 'yan bindiga sun kai wa rundunar sojin majalisar dinkin duniya hari a garin Timbuktu mai fama da kungiyoyin 'yan ta'adda daban-daban.

Bayan sojan Najeriya daya da ya mutu, karin wasu sojoji uku sun samu raunuka sakamakon harin 'yan bindigar.

Kazalika, wasu karin sojojin uku 'yan asalin kasar Chadi sun samu munanan raunuka a gabashin yankin Kidal mai makwabtaka da kasar Algeria bayan motar su ta taka wani sinadari mai fashe wa.

An kashe sojan Najeriya a kasar Mali
Rundunar sojoji
Asali: Facebook

Da yake Alla-wadai da kai wa rundunar sojin MDD hari tare da mika sakon ta'aziyya ga iyalan sojan da aka kashe, Guterres ya bayyana cewar irin wannan harin a karkashin laifukan yaki yake a dokar kasa da kasa.

DUBA WANNAN: 'Yan Boko Haram sun kai harin neman abinci a Askira-Uba, sun kone gidaje da shagunan jama'a

Tun bayan juyin mulkin da aka yi a Mali a shekarar 2012, kungiyoyin 'yan ta'adda masu nasaba da al-Qaeda suka samu gindin zama a arewacin kasar.

A shekarar 2013 ne MDD ta jibge rundunonin soji domin magance aiyukan kungiyoyin 'yan ta'adda a sassan kasar Mali. Ana yawan kai wa rundunonin soji dake arewacin kasar hare-hare, yayin da tsakiyar kasar ke fama da rigingimun kabilanci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel