Manyan jaruman Kannywood uku sun samu wata babban kwangila

Manyan jaruman Kannywood uku sun samu wata babban kwangila

Wasu manyan jaruman Kannywood da suka hada da Ali Nuhu, Usman Uzee da Maryam Booth sun zama wakilan kamfanin sufuri na CarXie.

Jaruman sun rattaba hannu kan yarjejeniyar amincewa da wakilcin ne tare da wakilan kamfanin da ranar Juma'a a Legas.

Kamar kamfanin Uber da Taxify, CarXie kamfanin sufuri ne na Najeriya da ke aiki a jihohin Najeriya da suka hada Legas, Abuja, Kaduna, Kano Awka da Enugu.

Manyan jaruman Kannywood uku sun samu wata babban kwangila
Manyan jaruman Kannywood uku sun samu wata babban kwangila
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yadda masu ciwon Ulcer za suyi azumin watan Ramadan cikin sauki - Masana

"Wannan sabon tsari ne daga kungiyar DuKAN, kwararen kamfanin fasaha na Najeriya. Kamfanin sufurin zai fadada ayyukansa zuwa wasu jihohin Najeriya," inji daya daga cikin sabbin wakilan kamfanin, Uzee.

Jaruman uku sune mutane ne farko da kamfanin ya dauka a matsayin wakilansa.

A hirar da tayi da Premium Times, Booth ta ce "Na rattaba hannu a kan kwangiloli guda biyu a wannan shekarar, daya da Airtel sannan na biyun da Ajinomoto. Ga kuma wannan na sake samu."

Booth kuma ta ce za tayi bidiyon tallata kamfanonin. "Zan kuma yi amfani da kafafen sada zumunta na wurin tallata hajojinsu da wasu abubuwan."

Masoya, da 'yan uwa da abokan arzikin jaruman sun rika taya mu murnar samun wannan cigaban ta shafinsu na Instagram.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Asali: Legit.ng

Online view pixel