Buratai ya yi banbami a kan mutuwar babban soja da wasu kananan sojoji a Borno

Buratai ya yi banbami a kan mutuwar babban soja da wasu kananan sojoji a Borno

Shugaban rundunar soji ta kasa, Laftanal Janar Tukur Buratai, ya bayyana kisan wani babban soja da wasu kananun sojoji biyu a jihar Borno, a matsayin kira ga rundunar soji da ta kara farka wa.

Buratai ya bayyana hakan ne ranar Talata a garin Maiduguri yayin jana'izar laftanal Kanal Ibrahim Aminu da kofural Jibril Ahmadu da Tijjani Mohammed, wadanda aka binne a makabartar sojoji ta maimalari.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) y rawaito cewar Aminu, kwamandan bataliyar soji ta 145, tare da ragowar sojojin biyu, sun gamu da ajalinsu ne bayan motar su ta taka wani bam da 'yan Boko Haram suka binne yayin sintiri.

Lamarin ya faru ne a kan titin Mauli zuwa Borgozo a karamar hukumar Kaga dake jihar Borno.

A jawabin sa, Buratai ya ce: "batun sinadarai masu fashe wa ba kankanuwar barazana ba ce, amma mu na daukan matakan kiyaye matsalar da suke haifar wa.

Buratai ya yi banbami a kan mutuwar babban soja da wasu kananan sojoji a Borno
Buratai
Asali: Twitter

"Babban kalubalen da muke fuskanta a yankin arewa maso gabas shine magance shirin makiyan rundunar soji dake kai musu hari ko binne musu sinadarai masu fashe wa. Yau ma gashi mun binne wasu da suka ras ran su sakamakon irin wannan kalubale da muke fuskanta.

"Akwai bukatar mu kara kula a kowanne lokaci domin tabbatar da mun kare kan mu daga annobar sinadarai masu fashe wa," a cewar Buratai.

DUBA WANNAN: Sojoji sun kashe masu zanga-zangar lumana 6 a Sudan

Ya bayyana mutuwar sojojin a matsayin babban takaici da bakin ciki.

Sannan ya kara da cewa: "Ina mika sakon ta'aziyya ga iyalin mamatan a kuma rundunar soji, musamman rundunar atisayen 'ofreshon lafiya dole. Ba kankanin rashi muka yi ba, zamu yi kewar su har abada."

Buratai ya bawa rundunar sojin tabbacin cewar kamfanin kera makamai na sojoji na daf da kammala kirkirar wata garkuwa da zata kare sojoji yayin fashewar bam da duk wani sinadari mai fashe wa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel