Rikicin masarautar Kano: Hakimin Bebeji yayi murabus

Rikicin masarautar Kano: Hakimin Bebeji yayi murabus

- Hakimin karamar hukumar Bebeji da ke jihar Kano, Haruna Sanusi yayi murabus

- Hakimin garin, wanda ke rike da mukamin Dan Galadiman Kano, ya sanar da murabus dinsa bisa dalili na rashin lafiya da kuma sauyin tsarin masarauta da aka samu kwanan nan

- Ganduje a ranar 8 ga watan Mayu ya samar da sabbin masarautu hudu da manyan sarakuna a jihar

Haruna Sanusi, Hakimin karamar hukumar Bebeji da ke jihar Kano yayi murabus daga mukaminsa, bisa dalili na rashin lafiya da kuma sauyin tsarin masarauta da aka samu kwanan nan.

Hakimin garin, wanda ke rike da mukamin Dan Galadiman Kano, ya sanar da murabus dinsa a wata wasika zuwa ga Sakataren gwamnati, mai kwanan wata 10 ga watan Mayu.

Gwamnan jihar Kano, a ranar 8 ga watan Mayu ya samar da sabbin masarautu hudu da manyan sarakuna a jihar, inda aka yi zargin cewa yana so ya karya darajar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ne.

Rikicin masarautar Kano: Hakimin Bebeji yayi murabus

Rikicin masarautar Kano: Hakimin Bebeji yayi murabus
Source: UGC

Legit.ng ta rahoto cewa Sarakunan da aka nada sune; Aminu Ado-Bayero, Bichi; Tafida Ila, Rano; Ibrahim Abdulkadir, Gaya da kuma; Ibrahim Abubakar ll, Karaye.

KU KARANTA KUMA: Rundunar soji ta ceto mata 29 da yara 25 daga yan ta’addan Boko Haram a Borno, hotuna

A ranar Juma’a, wata babbar kotun jihar Kano da ke zama a Ungogo ta yi umurnin hana gwamnan kacaccala masarautar.

Amma a ranar Asabar sai gashi gwamnan ya gabatar da wasikun nadi ga sabbin sarakunan, cewa bashi da masaniya akan umurnin kotun.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel