'Yar gidan Sarkin Kano ta mayarwa da Ganduje raddi
Yayin da gwamnan jiharKano Abdullahi Umar Ganduje ya kammala kacaccala jihar zuwa masarautu biyar, sai gashi diyar Sarkin Kano, Fulani Siddika ta yiwa gwamnan raddi akan abinda ya yiwa mahaifinta
Bayan kaddamar da karin masarautun yanka guda hudu a Kano da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi, 'yar gidan Sarkin Kano Muhammad Sanusi II ta yi wani raddi a shafinta na Instagram.
A bayanin da ta yi, duk da yake an goge, amma 'yar uwarta Fulani Siddika, ta sake sanyawa, inda ta bayyana gwamnan Kano Ganduje a matsayin "Bala'i da Allah ya kawowa mutanen Kano".

Asali: Facebook
Ga abinda ta ce a shafin nata:
"Idan kuna so ku ga me rashin asali ke jawo wa ku duba ku ga abinda Ganduje yake yi a Kano. Mutumin da bashi da wata daraja, amma yana kokarin ya ja da mutanen da suke da daraja. Ina addu'ar Allah yasa kada mahaifiyata ta ce na goge wannan bayanin a shafina. Ganduje shi ne bala'in da yafi komai a jihar Kano. Abinda yake yi a gwamnatinsa, son rai ne kawai a ciki. Bamu kamaci gwamnati irin wannan ba. Allah ya raba mu da masifar Ganduje dan kuwa mutanen da basu da asali sune suke bata masu asali."
KU KARANTA: Tashin hankali: wata guguwa ta yi sanadiyyar mutuwar mutane uku, ta lalata gidaje 200 a jihar Bauchi
Bugu da kari, Shahida ta kara rubuta cewa, "Da zarar Sarki ya tsorata da rasa kujerar sa, abinda yake yi shine ya sauke kansa,"
Babu shakka a cikin bayanin da ta yi a shafin nata Fulani Siddika, ta rubuta cewa:
"Ba ni da wani abu da zan cegaskiya!" 'Yar'uwata ce ta fada duka."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana
Asali: Legit.ng