Ganduje ya garzaya Abuja bayan yarimomin Kano 3 sun ki karban tayin zama sarkin Bichi

Ganduje ya garzaya Abuja bayan yarimomin Kano 3 sun ki karban tayin zama sarkin Bichi

Rahotanni sun kawo cewa akalla manyan yarimomin Kano uku ne suka ki amsa tayin zama sarkin Bichi, daya daga cikin sabbin masarautu hudu da gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya kafa a ranar 8 ga watan Mayu.

Majiyarmu ta tattaro cewa gwamnan ya yi wata ganawa Wamban Kano, Aminu Bayero; Chiroman Kano, Nasiru Bayero da hakimin Rao, Gaya da Karaye a gidan gwamnati a daren ranar Alhamis, 9 ga watan Mayu.

Majiyoyin cikin gida sun bayyana cewa an fara gabatar tayin zama sarkin Bichi ga Chiroman Kano Nasiru Bayero, amma sai yayi watsi da tayin.

Ganduje ya garzaya Abuja bayan yarimomin Kano 3 sun ki karban tayin zama sarkin Bichi
Ganduje ya garzaya Abuja bayan yarimomin Kano 3 sun ki karban tayin zama sarkin Bichi
Asali: UGC

Sannan sai gwamnan ya tura bukatar zuwa ga babban yayan Chiroma, Aminu Bayero, wanda yace yana bukaar lokaci domin tattaunawa. Majiyoyi na kusa da yariman sun bayyana cewa daga bisani sai shima ya ture tayin.

Ganduje ya sake tuntubar Galadiman Kano, Abbas Sanusi, mahaifin Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress, Abdullahi Abbas.

Alamu sun nuna cewa Galadima ma ba zai amshi tayin ba. Domin ya yi fushi da samar da kaarin masarautu a Kano.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa na kafa sabbin masarautu a Kano – Ganduje

An kuma tattaro cewa bayan yarimomin sun ki amsa tayin gwamnan, ya bar gurbin Bichi ba kowa.

Majiyoyin sun bayyana cewa a safiyar ranar Juma’a sai Ganduje ya bar Kano zuwa Abuja domin ganawa da mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo akan halin da jihar ke ciki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel