Dole na kammala aikin gadar Neja ta biyu a Kudu maso Gabas - Buhari

Dole na kammala aikin gadar Neja ta biyu a Kudu maso Gabas - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayin ziyarar duban aikin babbar gadar Neja ta biyu da ke birnin Onitsha a jihar Anambra, ya ce gwamnatin sa ta daura damarar ganin bayan aikin nan ba da jimawa ba cikin wa'adin ta na biyu.

Shugaban kasa Buhari wanda ya fara duban aikin tun daga birnin Asaba tare da gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya ce aikin gadar Neja wani babban ginshiki ne na bunkasar tattalin arziki a yankin Kudu maso Gabas da kuma Najeriya baki daya.

Aikin gadar Neja
Aikin gadar Neja
Asali: Twitter

Aikin gadar Neja
Aikin gadar Neja
Asali: Twitter

Aikin gadar Neja
Aikin gadar Neja
Asali: Twitter

Aikin gadar Neja
Aikin gadar Neja
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, a yayin da shugaban kasa Buhari ke ci gaba da shafe hutun kwanaki goma a birnin Landan na kasar Birtaniya, mataimakin sa, Farfesa Yemi Osinbajo, shi ne ya yi wakilcin sa yayin ziyarar duban aikin gadar Neja da ya kai yankin Kudu maso Gabashin kasar nan.

Mataimakin shugaban kasa Osinbajo wanda tawagar sa ta hadar da Ministan makamashi, ayyuka da gidaje, Babatunde Raji Fashola, ya bayyana farin cikin sa tare da yabawa kwazon Injiniyoyi masu cin kwangilar katafaren aikin.

KARANTA KUMA: Kotu ta kwace kadarori 214 daga hannun barayin gwamnati saba'in

Osinbajo ya kuma ziyarci kasuwar Akwa da ke jihar Anambra inda ya yi tsokaci ga 'yan kasuwa masu ribatar shirin bayar da tallafin hannun jari na TraderMoni da ya kasance daya daga cikin jerin shirye-shirye hudu na inganta jin dadin al'umma da gwamnatin su ta dabbaka

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel