Yadda APC za Ta Karya Lagon Peter Obi a Zaben 2027

Yadda APC za Ta Karya Lagon Peter Obi a Zaben 2027

  • Jam’iyyar APC a jihar Legas ta ce za ta yi duk mai yiwuwa domin hana Peter Obi sake kayar da Bola Tinubu a zaben shugaban kasa na 2027
  • Shugaban APC na jihar, Cornelius Ojelabi, ya bayyana cewa kayen da jam’iyyar ta sha a Legas a zaben 2023 ya zama darasi a gare ta
  • Ojelabi ya kuma goyi bayan kawancen siyasa na Rainbow Coalition, yana mai cewa kungiyoyi daban-daban sun hada kai domin ganin Tinubu ya zarce

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Legas – Jam’iyyar APC reshen jihar Legas ta sha alwashin hana dan takarar NDC, Peter Obi sake samun nasara a jihar a zaben 2027.

Shugaban APC na jihar, Cornelius Ojelabi, ya ce jam’iyyar ta koyi darasi daga kayen da ta sha a zaben baya, kuma ta fara shirye-shiryen ganin Shugaba Bola Tinubu ya sake lashe zabe.

Kara karanta wannan

Matsaloli 10 da Sheikh Isa Pantami ya tsallake wajen zama ‘dan takarar gwamna a Gombe

Peter Obi na NDC
Dan takarar NDC, Peter Obi. Hoto: Mr Peter Obi
Source: Facebook

Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da jaridar Punch, inda ya ce APC ba ta daukar komai da wasa duk da kasancewarta jam’iyya mai mulki.

APC ta ce ta kara kaimi

Ojelabi ya ce ana ganin yadda APC ke gudanar da harkokin siyasa da hada kan magoya bayanta a jihohi da kananan hukumomi daban-daban gabanin zaben shugaban kasa na ranar 16 ga Janairu, 2027.

Ya ce jam’iyyar na tuntubar masu kada kuri’a domin bayyana musu nasarorin da gwamnatin Tinubu ta samu cikin shekaru uku da rabi da ta yi a mulki.

Shugaban ya ce kasancewarsu jam’iyya mai mulki ba yana nufin za su yi sakaci ba, domin suna son masu zabe su fahimci abin da gwamnati ta cimma tare da yanke shawarar goyon bayanta a akwatin zabe.

Magana kan Peter Obi

Da aka tambaye shi matakan da APC ta dauka domin hana Peter Obi sake samun nasara a Legas, Ojelabi ya nuna kwarin gwiwar cewa jam’iyyar za ta fi abin da ta yi a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Abokin takaran Atiku ya bayyana dalilin rabuwa da shi ya kama layin Tinubu a APC

Ya ce kayen da APC ta sha a lokacin ya zama abin fadakarwa gare su, musamman ganin cewa Legas ita ce kadai jiha a Najeriya da jam’iyya daya ta ci gaba da mulki tun shekarar 1999.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Tinubu a ofis. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Sai dai ya ki bayyana takamaiman dabarun da jam’iyyar za ta yi amfani da su wajen dakile Obi, yana mai cewa za su fi mayar da hankali kan ayyukan gwamnatin da kuma neman kuri’un jama’a.

Ojelabi ya kuma bayyana goyon bayansa ga kawancen Rainbow Coalition da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ke ingantawa.

Ya ce ko da akwai kawance ko babu, masu ruwa da tsaki a siyasar kasar suna magana ne da murya daya wajen ganin Tinubu ya koma fadar shugaban kasa a 2027.

Akpabio zai samawa Tinubu kuri'u

A wani labarin, kun ji cewa shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yi hasashen cewa Tinubu zai samu sama da kuri’u miliyan biyu a jihar Akwa Ibom.

Akpabio ya bayyana hakan ne a wani gangamin APC da aka gudanar a Uyo, inda ya ce sama da masu zabe miliyan biyu a jihar sun karbi katin zabe na dindindin (PVC).

Hakan na zuwa ne yayin da jam'iyyar APC ke kara shirye-shiryen tunkarar zaben shugaban kasa na 2027, inda ta ke gudanar da yakin neman zabe a jihohi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng