Sarakunan Yarbawa a Jihohin Arewa 19 Sun Dauki Babban Alkawari ga Tinubu

Sarakunan Yarbawa a Jihohin Arewa 19 Sun Dauki Babban Alkawari ga Tinubu

  • Shugaban Majalisar Sarakunan Yarbawa a jihohin Arewa 19 da Abuja, Ambasada Muhammad Arigbabuwo, ya bukaci ’yan Najeriya su hada kai wajen mara wa Tinubu baya a 2027
  • Ya ce dole ne ’yan Najeriya su ajiye bambance-bambancen addini da kabila domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban kasa
  • Fasto Moses Chooji ya ce Tinubu ya aza harsashin ci gaban Najeriya, don haka ya kamata a ba shi damar kammala ayyukan da ya fara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya da Manyan Yarbawa a jihohin Arewa 19 da Abuja sun yi wa Bola Tinubu alkawari.

Shugaban majalisar, Ambasada Muhammad Arigbabuwo, ya bukaci ’yan Najeriya su hada kai domin marawa Tinubu baya a kokarinsa na neman wa’adi na biyu a zaben 2027.

Kara karanta wannan

"Abin da zai sa Tinubu ya samu gagarumar nasara a zaben shugaban kasa na 2027"

Sarakuna za su ba Tinubu ƙuri'u a Arewa
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Dada Olusegun.
Source: Facebook

Sarakuna sun yi wa Tinubu alkawari

Arigbabuwo ya yi wannan kira ne yayin wani babban taron nuna goyon baya ga Tinubu da kungiyar Grant Ecosystem Subscribers ta shirya a Kaduna, cewar Leadership.

An gudanar da taron ne karkashin taken Renewed Hope Agenda: Consolidating Unity and Victory for APC 2027, inda sarakunan gargajiya, shugabannin addinai da kungiyoyin siyasa suka halarta.

Sarkin ya ce ci gaban Najeriya ya dogara ne da yadda al'ummarta za su iya kawar da bambancin kabila da addini, yana mai cewa hadin kan kasa shi ne ginshikin zaman lafiya da ci gaba mai dorewa.

Ya kuma yabawa Tinubu bisa abin da ya bayyana a matsayin jarumtaka, hangen nesa da salon shugabancinsa wajen fuskantar kalubalen kasar.

Arigbabuwo ya kuma yaba da gudunmawar mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, da ministocin tarayya da sauran masu ruwa da tsaki wajen aiwatar da manufofin gwamnatin.

An yi wa Tinubu alkawarin kuri'u a Arewa
Shugaba Bola Tinubu yana dagawa yan Najeriya hannu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

An bukaci a ba Tinubu damar kammala wa’adinsa

Kara karanta wannan

Abokin takaran Atiku ya bayyana dalilin rabuwa da shi ya kama layin Tinubu a APC

A nasa jawabin, Fasto Moses Terkaa Chooji, wanda aka fi sani da Rev. Moses daga Abuja, ya bukaci ’yan Najeriya su tantance gwamnatin Tinubu bisa ayyukanta da kokarin da take yi wajen ci gaban kasa.

Ya ce a cikin shekaru uku da rabi da Bola Tinubu ya yi a kan karagar mulki, ya fara aza harsashin gina Najeriya mai wadata, don haka ya kamata a ba shi damar kammala abin da ya fara.

Faston ya kuma bukaci mazauna jihohin Filato, Kwara, Nasarawa, Neja da Kogi su shiga cikin harkokin zabe tare da karfafa goyon bayansu ga Tinubu a 2027.

Ya yi ikirarin cewa kungiyar Grant Ecosystem ta samo asali ne daga ayyukan bayar da tallafi a shekarun 2015 zuwa 2016, inda ya ce tana da mambobi tsakanin miliyan 130 zuwa 150 a shiyyoyin siyasar Najeriya shida.

An bukaci sauya tsarin tattalin arzikin Najeriya

A nasa jawabin, Apostle Charles Oke ya yi kira da a sauya tsarin tattalin arzikin Najeriya daga dogaro da rabon kudaden shiga zuwa bunkasa masana'antu, fasaha da sarrafa kayayyaki.

Ya yi nuni da sauyin tattalin arzikin kasar China, yana mai cewa tsare-tsare masu kyau da bunkasa masana'antu za su taimaka wajen samar da ayyukan yi da inganta rayuwar al'umma.

Kara karanta wannan

An yi gamon katar: Abin da Tinubu ya fada wa Fubara bayan APC ta hana shi takara

Dan Atiku ya dage kan zaben Tinubu

An ji cewa Abba Atiku ya jagoranci ƙungiyarsa ta Haske zuwa Jigawa, kuma ya narkar da ita cikin APC domin goyon bayan Bola Tinubu.

Ƙungiyar ta ce za ta mara wa shugaban Najeriya baya a zaɓen 2027 domin ya kammala wa'adin shekaru takwas a kan karagar mulki.

Gwamnan Jigawa, Umar Namadi, ya yabi aikin Abba, ya yi alƙawarin haɗa kai da ƙungiyar domin ganin APC ta yi galaba a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.