'Yan bindiga sun kai hari gidan tsohon gwamnan jihar Sokoto Attahiru Bafarawa

'Yan bindiga sun kai hari gidan tsohon gwamnan jihar Sokoto Attahiru Bafarawa

Wasu da ake zargin cewar 'yan bindiga ne sun kai hari gidan tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa, dake mahaifar sa; garin Bafarawa, tare da kashe maigadin gidan, Abdullahi Jijji.

Harin na zuwa ne a cikin kasa da sa'o'i 24 bayan tsohon gwamnan ya kaddamar da wata gidauniya domin taimakon jama'ar da harin 'yan bindiga ya shafa a arewacin Najeriya, musamman a jihar Sokoto.

Kazalika, 'yan bindigar sun sace wani 'da ga dan uwan tsohon gwamnan da ke zaune a gidan da suka kai harin.

Da yake tabbatar da kai harin, babban darekta a gidauniyar da Bafarawa, Dakta Sulaiman Shu'aibu Shinkafi, ya ce an kai harin ne da misalin karfe 9:00 na daren ranar Juma'a.

'Yan bindiga sun kai hari gidan tsohon gwamnan jihar Sokoto Attahiru Bafarawa
Tsohon gwamnan jihar Sokoto Attahiru Dalhatu Bafarawa
Asali: Twitter

Ya ce 'yan ta'addar sun dira a gidan tsohon gwamnan cikin wani salo irin na kwararrun 'yan bindiga da aka saba gani a shirin fim tare da yin barazanar rushe kauyukan Bafarawa da Kamarawa da daukacin karamar hukumar Isa da ke jihar Sokoto.

DUBA WANNAN: Bafarawa ya zayyana illolin da rashin tsaro ke yiwa tattalin arzikin Najeriya

Shinkafi ya kara da cewa, 'yan bindigar da suka zo garin a kan babura, sun tsaya sun sayi man fetur a garin kafin su wuce su kai hari a gidan tsohon gwamnan.

Da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Sokoto, DSP Muhammad Sadiq, ya ce basu da masaniyar kai hari a gidan na Bafarawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel