Yankin Kudu maso Gabas ne ya dace su fitar da shugaban kasa a 2023 - Balarabe Musa

Yankin Kudu maso Gabas ne ya dace su fitar da shugaban kasa a 2023 - Balarabe Musa

- Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Balarabe Musa ya ce lokaci ya yi da ya dace yankin Kudu maso Gabas su fitar da shugaban kasa a 2023

- Musa ya yi bayyani cewa dukkan yankunan kasar nan sun fitar da shugaban kasa illa yankin na Kudu maso Gabas

- Tsohon gwamnan ya ce duk wanda ya yi yunkurin hana yankin damar fitar da shugaban kasa baya neman zaman lafiya

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Balarabe Musa ya ce lokaci ya yi da ya dace a bawa yankin Kudu maso Gabashin Najeriya damar fitar da shugaban kasa a shekarar 2023.

Musa ya ce dukkan sauran sassan Najeriya sun fitar da shugaban kasa tun da aka koma mulkin demokradiyya a 1999 amma banda yankin Kudu maso Gabas. Ya kara da cewa duk wanda baya son yankin ta fitar da shugaban kasa mutum ne mai son rikici.

Yankin Kudu maso Gabas ne ya dace su fitar da shugaban kasa a 2023 - Balarabe Musa
Yankin Kudu maso Gabas ne ya dace su fitar da shugaban kasa a 2023 - Balarabe Musa
Asali: Depositphotos

Dattijon ya yi wannan jawabin ne a wata hira da ya yi da Daily Sun inda ya ce yankin arewa ta fitar da shugabanin kasa lokuta da dama kuma yankin Kudu maso Yamma da Kudu maso Kudu sunyi sau daya saboda haka lokaci ya yi da za a bawa Kudu maso Gabas dama.

DUBA WANNAN: Daukan doka a hannu: Anyi artabu tsakanin 'yan sanda da 'yan kungiyar sintiri a Katsina

Ya ce: "Munyi magana a kan tsarin karba-karba da kishin yanki kuma munyi magana a kan yankun hudu na Najeriya - Arewa, Kudu maso Yamma, Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu.

"Arewa sunyi mulki sau da yawa, yankin Kudu maso Yamma da Kudu maso Kudu sunyi sau daya saboda haka lokaci ya yi da za a bawa Kudu maso Gabas dama. Mene zai hana a bawa yankin dama domin su san ana damawa da su kuma mu samu zaman lafiya?

"Wannan shine adalci. Mene zai sa wani ya ce dole sai an samu shugaban kasa daga Arewa kuma ko Kudu maso Yamma ko Kudu maso Kudu? Masu irin wannan ra'ayin basu son zaman lafiya.

"Ba za mu sake maimaita kuskuren da mukayi a 1999, 2007, 2011 da sauran shekarun ba saboda yankunan Arewa, Kudu maso Yamma da Kudu maso Kudu suna gabatar da 'yan takara ne da sunan tsarin karba-karba.

"Wannan lokacin abubuwa za su canja, ya dace dukkan 'yan Najeriya su hada kai wuri guda su zabi shugaban kasa daga Kudu maso Gabas domin samun maslaha."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel