Gwamnatin Jigawa ta sha alwashin biyan N30,000 mafi karancin albashi

Gwamnatin Jigawa ta sha alwashin biyan N30,000 mafi karancin albashi

- Jihar Jigawa ta nuna shirinta na biyan N30,000 a matsayin mafi karancin albashi

- Mataimakin gwamnan jihar, Ibrahim Hassan Hadejia ya bayyana cewa tuni sun kammala shiri domin biyan Karin albashi na ma’aikata a jihar

Gwamnatin jihar Jigawa a jiya Litinin, 29 ga watan Afrilu ta nuna shirinta na biyan N30,000 a matsayin mafi karancin albashi.

Mataimakin gwamnan jihar, Ibrahim Hassan Hadejia ya bayyana hakan yayinda yake amsa tambayoyi daga manema labarai a garin Dutse, babbar birnin jihar.

Gwamnatin Jigawa ta sha alwashin biyan N30,000 mafi karancin albashi
Gwamnatin Jigawa ta sha alwashin biyan N30,000 mafi karancin albashi
Asali: UGC

Yace tuni gwamnatin jihar ta yi shirin biyan Karin albashin ma’aikatan a kasafin kudin kudin 2019.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa a jiya Alhamis ne 25 ga watan Afrilu kungiyar kwadago ta kasa ta gargadi cewa babu wata jiha a kasar nan da za ta karbi karancin albashi da ya yi kasa da N30,000.

KU KARANTA KUMA: Jagorancin majalisa ta 9: PDP na shirya kaidin zaben Goje da Ekweremadu

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa shugaban kungiyar kwadagon ta kasa, Mista Ayuba Wabba, shine ya fitar da sanarwar a garin Ado Ekiti, babban birnin jihar Ekiti, yayin da yake jagorantar zaben shugaban kungiyar kwadagon na jihar.

Ya bayyana cewa kungiyar kwadago ta kasa ta bai wa ma'aikatan Najeriya umarnin kada su karbi karancin albashin da ya yi kasa da N30,000 daga wurin kowanne gwamna a Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel