Jami'an KASTELEA sun kashe mutum guda, sun raunata wani a Zaria

Jami'an KASTELEA sun kashe mutum guda, sun raunata wani a Zaria

Ana zargin wasu daga cikin jami'an hukumar kula da cunkuson ababen hawa da tabbatar da dokar tsaftar muhalli a jihar Kaduna (KASTELEA) da kisan wani dan Acaba tare da raunata wasu mutum biyu a Zaria.

Wani bincike da wakilin kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya gudanar, ya nuna cewar jami'an KASTELEA da aka jibge a Tudun Wada ne suka haddasa hatsarin da ya kashe dan acaban tare da raunata wasu mutane biyu.

Wani shaidar gani da ido ya shaida wa NAN cewar jami'an KASTELEA sun biyo wani dan acaba daga Tudun Wada, kuma sun cimma sa a kwanar Alhudahuda da ke garin Zaria.

"Sun tsayar da shi ne amma sai ya ki tsaya wa, sai suka biyo shi a motar su. Ba su same shi ba sai a daidai wurin juya wa (U-turn) na kwanar Alhuahuda, inda suka sha gabansa da mota sannan suka take shi bayan ya fadi," a cewar sahaidar.

Jami'an KASTELEA sun kashe mutum guda, sun raunata wani a Zaria
Jami'an KASTELEA da gwamna El-Rufa'i
Asali: Twitter

Sanna ya kara da cewa,"wani mai Keke Napep ya zo ya doki motar jami'an na KASTELEA, lamarin da ya saka direban da wata fasinja daya suka samu raunuka."

NAN ta ce ba a bayyana sunan dan acabar da ya mutu ba har ya zuwa lokacin da aka wallafa wannan rahoto. Sai dai, ta bayyana cewar an garzaya da wadanda suka samu rauni zuwa asibitin koyar wa na jami'ar Ahmadu Bello da ke Tudun Wada a Zaria domin a duba lafiyar su.

DUBA WANNAN: Da duminsa: Buhari ya saka ranar sallamar dukkan ministoci da hadiman sa

Kazalika, NAN ta rawaito cewar mutuwar dan acaban ta dugunguzuma abokan sana'ar sa, wadanda suka yi dandazon zuwa fadar sarkin Zaria, Dakta Shehu Idris, domin kai kukan su.

Da yake jawabi ga dandazon 'yan acabar bayan kammala wata gana wa da sarkin Zaria, shugaban karamar hukumar Zaria, Alhaji Aliyu Idris, ya bukaci matasan da su kwantar da hankalin su tare da daukar musu alkawarin cewar za a gudanar da bincike a kan abinda ya faru, sannan a dauki mataki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel