Abin da Tinubu yake so shi ne ya rike madafan ikon Najeriya – Dogara

Abin da Tinubu yake so shi ne ya rike madafan ikon Najeriya – Dogara

Shugaban majalisar wakilan tarayya a Najeriya, Rt. Hon Yakubu Dogara, yayi magana a kan zargin da babban jagoran nan na jam’iyyar APC mai mulki Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya jefe sa da shi.

A cikin ‘yan kwanakin nan ne Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya fito yace shugabannin majalisar tarayya sun rika yin cushe da bata lokaci wajen aikin kasafin kudi har su ka rika kara wasu ayyukan da ba za su amfani kowa ba illa karen kan-su.

Yakubu Dogara ya karyata wannan zargi inda ya kuma koka da wannan jawabi na Bola Tinubu wanda yace babu kanshin gaskiya a cikin sa. Dogara yake cewa abin da Tinubu yake so shi ne ya ga yayi karfa-karfa a kowane bangaren kasar.

A martanin Kakakin majalisar wakilan ta bakin wani Hadimin sa mai suna Turaki Hassan, ya fito yace bai yi tunanin Tinubu zai buge da sheka karya da boye gaskiya domin kurum ganin ya mamaye duk wasu madafan iko na kasar nan ba.

KU KARANTA: 'Diyar Abba Kyari ta samu shiga cikin gwamnati a boye

Rt. Hon. Dogara yake cewa yayi aikin da ya zarce na Tinubu wajen ganin gwamnatin Buhari ta tsaya da kafafunta. Dogara yake cewa Tinubu yana nunawa Duniya cewa yana tare da Buhari ne amma yana yi wa gwamnatin nan saran mummuke.

Shugaban majalisar ya fayyace cewa shugaba Buhari ya gabatar da kundin kasafin 2015 ne yayin da ake saura kwana 9 shekarar ta kare gaba daya, haka kuma aka yi a 2016 da 2018 inda aka rika kawo kundin kasafin a tsakiyar Watan Disamba.

Hassan yake cewa kin rattaba hannu da shugaban kasa Buhari yayi a kudirin majalisa da kuma kudirin yi wa tsarin mulki garambawul yana cikin abin da ya sa ake daukar lokaci kafin a amince da kasafin kudi a Najeriya wanda sai an bi diddiki.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel