Zakaran da Allah Ya nufa da cara: An tsinci jariri bayan mahaifiyarsa ta wullashi cikin rijiya

Zakaran da Allah Ya nufa da cara: An tsinci jariri bayan mahaifiyarsa ta wullashi cikin rijiya

Rundunar Yansandan jahar Jigawa sun sanar da gano wani dan jariri sabon haihuwa daga cikin wata tsohuwar rijiya da ake kyautata zaton mahaifiyarsa ce ta jefar dashi a cikin rijiyar da nufin halakashi, amma Allah bai yi ba.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin rundunar Yansandan jahar, SP Audu Jinjiri ne ya bayyana haka a ranar Litinin, 22 ga watan Afrilu a garin Dutse, inda yace an gano wannan jariri ne a wata tsohuwar rijiya dake cikin karamar hukumar Kaugama.

KU KARANTA: Alheri gadon barci: Attajiri ya fara rabon kayan Sallah ga gajiyayyu da talakawa a Sakkwato

“Da misalin karfe 4 na ranar 20 ga watan Afrilu ne wani mutumi mai shekaru 40, Abdul Aziz Lawan, wanda shine dakacin kauyen Kuka-kwance ya kai wannan jariri zuwa caji ofis dake karamar hukumar Kaugama.

“Yace ya gano jaririn ne kwance a cikin wata tsohuwar rijiya, kuma daga dukkan alamu ana haihuwarsa aka jefar dashi a cikin rijiyar. Bayan jami’anmu sun karbeshi sai suka garzaya dashi Asibiti don duba lafiyarsa, inda aka tarar dashi yana cikin koshin lafiya.” Inji shi.

Daga karshe kaakakin yace sun kaddamar da bincike akan wannan lamari don gano wanda ya aikata wannan danyen aiki na yunkurin kashe wannan jariri ta hanyar jefar dashi a cikin rijiya da gangan, tare da tabbatar da an hukunta ko waye.

Irin wannan lamari na jefar da jarirai ya zama ruwan dare a tsakanin Musulmai mazauna yankin Arewacin Najeriya, inda yawanci hakan na faruwa sakamakon samunsu da ake yi ta hanyar zinace zinace, don haka sai iyaye ko uwar, ko kuma uban su jefar da yaron wai don gudun abin kunya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel