Abinda ya sa kasashen da suka cigaba basa son taimakon Najeriya - Buhari

Abinda ya sa kasashen da suka cigaba basa son taimakon Najeriya - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce wasu daga cikin kasashen da suka cigaba basa son taimakon Najeriya ne saboda kuskuren tunanin cewar Najeriya kasa ce mai arziki.

A cewar jawabin da Garba Shehu, kakakin shugaban kasa, ya fitar a ranar Alhamis, shugaba Buhari ya fadi hakan ne yayin karbar takardun fara aiki na jakadun kasashe uku da suka hada da Indiya, Kuwait da Namibia a Abuja.

Shugaba Buhari ya fada wa jakadan kasar Kuwait, Al Bisher, cewar, "an kwakuba Najeriya cikin kasashen duniya masu arzikin man fetur, ta zama mamba a kungiyar kasashen duniya masu sayar da danyen man fetur a kasuwar duniya (OPEC).

Abinda ya sa kasashen da suka cigaba basa son taimakon Najeriya - Buhari

Buhari
Source: Facebook

"Sannan goyon bayan wasu daga cikin manufofin kasashen kungiyar OPEC, a wasu lokutan, ya na hana kasashen da suka cigaba taimakon Najeriya bisa kuskuren tunanin cewar Najeriya kasa ce mai arziki." a cewar jawabin.

DUBA WANNAN: Kotu ta tsige Sanatan APC, ta ce dole ya biya albashi da alawus din da ya karba cikin mako 2

Sannan ya kara da cewa "Najeriya za tayi murna da taimako a bangaren ilimi, fasaha, da aiyukan raya kasa da za su inganta rayuwar jama'a."

A martanin sa, Al Bisher ya kasar Kuwait ba ta saka Najeriya cikin kasashen Afrika da ta ke yiwa aiyukan raya kasa ba a karkashin shirin 'Kuwait Project' da suka kirkira a kasashen Afrika a shekarar 1961. Ya kara da cewa amma yanzu za a saka Najeriya cikin jerin kasashen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel