‘Yan APC da-dama sun gaza samun tazarce a Jihar Nasarawa

‘Yan APC da-dama sun gaza samun tazarce a Jihar Nasarawa

- 6 daga cikin ‘Yan Majalisar jihar Nasarawa ne su ka zarce a zaben 2019

- APC ta lashe kujeru har 15 a Majalisar dokokin Jihar yayin da PDP ta ci 7

- Jam’iyyun adawa SDP da LP sun lashe kujeru 2 a zaben jihar Nasarawa

Labari ya zo mana cewa ‘Yan majalisar dokoki na jihar Nasarawa 6 ne kurum su ka samu zarcewa a kan kujerarsu a zaben 2019 da aka yi bana. Daga cikin wadanda su ka zarce akwai Mai girma kakakin majalisar dokoki na jihar.

‘Yan majalisun APC da ke kan kujerun a yanzu, ba su iya sake darewa kan mulki ba. Fitattun ‘Yan majalisar APC da su kayi sa’ar lashe zaben na bana sun hada Honarabul Ibrahim Balarabe-Abdullahi da kuma Mohammed Okpoku.

KU KARANTA: Shugaban kasa Buhari zai sallami wasu Ministocinsa

Ibrahim Balarabe-Abdullahi shi ne shugaban majalisar jihar a yanzu kuma shi ne mai wakiltar yankin Umaisha da Ugya. Okpoku kuma shi ne ‘dan majalisar da ke wakiltar mazabar Udege da Loko a majalisar dokoki na jihar.

Sauran ‘yan majalisar na APC da su kayi dace su ka iya lashe zabe a jam’iyyar mai mulki sun hada da Daniel Ogazi na yankin Kokona da kuma Tanko Tanko, da Ibrahim Muluku da su ke wakiltar Biranen Lafiya da cikin Garin Nasarawa.

Kamar yadda labari ya zo mana jam’iyyar nan ta SDP da kuma LP sun lashe kujeru 2 a zaben jihar Nasarawa. Wadannan jam’iyyun hamayya sun yi nasarar tsaida ‘yan majalisa yayin da PDP ta samu ‘yan majalisa 7 a zaben na 2019.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel