Gobara ta kone shaguna 35 a babbar kasuwa a Kano

Gobara ta kone shaguna 35 a babbar kasuwa a Kano

- An samu tashin gobara a 'Yan nama da ke kasuwar Kurmi a birnin Kano

- A cewar kakakin hukumar kashe gobara a jihar Kano, Alhaji Saidu Mohammed, gobarar ta kone shaguna a kalla 35

- Mohammed ya bawa 'yan kasuwa shawarar su kara lura soasai tare da kiyaye wa wajen amfani da duk wasu kayayyaki da kan iya haddasa gobara

Hukumar kashe gobara a jihar Kano ta ce a kalla shaguna 35 suka kone sakamakon wata gobara da tashi a 'Yan nama da ke cikin kasuwar Kurmi.

Alhaji Saidu Mohammed, kakakin hukumar, ne ya tabbatar da faruwar hakan yayin da yake magana da wakilin kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) yau, Lahadi, a Kano.

Ya ce gobarar ta kone shaguna 27 kurmus, yayin da kone sassan wasu shaguna 8.

Gobara ta kone shaguna 35 a babbar kasuwa a Kano

Gobara ta kone shaguna 35 a babbar kasuwa a Kano
Source: UGC

"Da misalin karfe 4:56 na safe wani mutum mai suna Ado Musa ya kira mu tare da sanar da mu cewar gobara ta tashi a kasuwar.

"Nan da nan muka aika jami'anmu da motocin kashe gobara, sun isa wurin da misalin karfe 5:03 domin hana wutar gobarar yaduwa zuwa sauran shaguna," a cewar sa.

DUBA WANNAN: An bawa hammata iska tsakanin Abdullahi Abbas da Kwankwaso

Ya bawa 'yan kasuwa shawarar su kasance masu kula sosai da kuma kiyaye wa wajen amfani da duk wasu kayayyaki da kan haddasa tashin wuta domin gudun sake samun afkuwar irin wannan hatsari.

Sannan ya kara da cewa har yanzu ana gudanar da bincike domin gano silar tashin gobarar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel