Takaitacen tarihin Marigayi Justice Mamman Nasir

Takaitacen tarihin Marigayi Justice Mamman Nasir

An haifi Jastis Nasir a shekarar 1929 a jihar Katsina. Ya yi karatun makarantar sakandire a Kaduna, inda ya samu takardar shaidar kammala karatun sakandire ta kasashen yammacin Afrika (WAEC) a shekarar 1947.

Marigayin ya halarci jami'ar Ibadan kafin daga bisani ya wuce kasar Ingila, inda ya kammala karatunsa na digiri a bangaren shari'a a shekarar 1956.

Bayan dawowarsa Najeriya a shekarar 1956, an nada shi a matsayin alkali kafin daga bisani a nada shi a matsayin minista shari'a, na yankin arewacin Najeriya, a shekarar 1961, mukamin da ya rike na tsawon shekaru biyar.

Takaitacen tarihin Marigayi Justice Mamman Nasir
Takaitacen tarihin Marigayi Justice Mamman Nasir
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Shugabancin majalisa: Lawan ya bijrewa umurnin Oshiomhole, ya nemi goyon bayan 'yan PDP

A shekarar 1967 ne aka nada shi a matsayin darektan sashen gurfanarwa na yankin arewa kafin daga bisani ya zama mai kula da shari'a a yankin arewa ta tsakiya, mukamin da ya rike har zuwa lokacin da aka nada shi a matsayin daya daga cikin alkalan kotun koli a shekarar 1975.

A shekarar 1978 ne aka nada shi a matsayin shugaban kotunan daukaka kara na Najeriya, mukamin da ya rike har zuwa lokacin da ya yi ritaya a shekarar 1992,shekarar da aka nada shi a matsayin Galadiman masarautar Katsina.

Ya kuma rasu ranar Asabar 13 ga watan Afrilun 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164