In kana da rai kasha kallo: An kama wani yaro yana cire kudi a ATM ba tare da kati ba
- An cafke wani karamin yaro da ya saba zuwa ATM ya cure kudi ba tare kati ba
- Yaron ya bayyana cewa ya na da wata lamba da idan ya saka zai cire kudi ko nawa ne ba tare da ya yi amfani da kati ba
Wani abin mamaki da ya faru a jiya Talata 9 ga watan Afrilu, a wani injin cire kudi (ATM), na wani banki a kusa da gidan rediyon Najeriya, da ke Dugbe, cikin jihar Ibadan, inda aka kama wani matashin yaro yana cire kudi a injin cire kudin ba tare da amfani da katin cire kudi ba.
Matashin yaron, mai suna Azeez Morufu, ya ce ba wannan ne karo na farko da ya fara cire kudi ba tare da katin cire kudin ba.
A lokacin da ya ke magana da ma'aikatan gidan rediyon Najeriya, Morufu ya ce ya na da wata lamba da ya ke amfani da ita a duk lokacin da ya ke bukatar kudi zai je injin cire kudi (ATM) ya saka zai ciri iya kudin da ya ke bukata ya tafi abinshi.
Asirin Morufu ya tonu ne a dai dai lokacin da wani mutumi ya zo wucewa ta gaban bankin, ya ga Morufu da makudan kudade a gaban injin cire kudin.
KU KARANTA: Bankin musulunci ya bawa gwamnatin Najeriya dala miliyan 532
Mutumin ya bayyana cewa lokacin da ya ga Morufu ya ji zargi ya shiga ranshi, ganin kayan da ke jikin shi sunyi datti, sannan kuma ga yarinta a tattare da shi, kuma ya ga ya na cire kudi masu yawa a inji. Mutumin ya ce tun lokacin ya ji ranshi ya kasa aminta da yaron.
A karshe dai an mika yaron zuwa ga hukumar 'yan sanda ta jihar domin gabatar da bincike akan shi.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng