Shugaba Buhari ya bar Dubai, an yi masa bikin bankwana (Bidiyo)

Shugaba Buhari ya bar Dubai, an yi masa bikin bankwana (Bidiyo)

Shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da tawagar sa sub bar kasar Dubai domin dawowa gida Najeriya bayan kammala halartar wani taro a kan harkokin kasuwanci da saka hannun jari na kwana biyu da aka yi a Dubai.

Buhari da wasu minitocinsa da gwamnoni da hadimai sun bar Najeriya ne ranar Lahadi zuwa kasar Qatar kafin daga bisani ya zarce zuwa kasar kasar hadaddiyar Daular larabawa, da aka fi sani da Dubai.

A yayin da shugaba Buhari ya kammala halartar tarukan da suka kai shi kasar ta Dubai, sannan kuma ya gana da shugabannin kasar, an shirya biki na musamman domin yi masa bankwana kafin ya shiga jirginsa.

Duba faifan bidiyon bikin a nan:

Yayin da yake kasar Dubai, shugaba Buhari ya gana da kungiyoyi 6 na masu saka hannun jari bayan kammala taron masu saka hannun jari na wannan shekara da aka yi a Dubai.

A jawabin da Femi Adesina, kakakin shugaban kasa ya fitar, Buhari ya aika sako daya ga masu saka hannun jarin: "Ku zo Najeriya domin samun riba a kasuwancinku cikin kankanin lokaci."

Sheikh Ahmed Al Maktoum, dan cikin gidan sarautar kasar Dubai kuma daya daga cikin masu saka hannu jari, ya nuna sha'awarsa ta kafa cibiyar samar da hasken wutar lantarki a Legas.

Shugaba Buhari ya bar Dubai, an yi masa bikin bankwana (Bidiyo)
Shugaba Buhari a kasar Dubai
Asali: Facebook

Mista Yusuff Ali, shugaban kamfanin 'Lulu Group' masu manyan shagunan kayan sayar wa a yankin gabsa ta tsakiya da Asia, ya nuna sha'awarsa ta hada gwuiwa da manoma a Najeriya domin samun kayan amfanin gona masu inganci da tsafta. Rukunin shagunan 'Lulu' na da ma'aikata fiye da 50,000.

DUBA WANNAN: Akwai sarakuna da ke hada baki da 'yan bindiga a Zamfara - Ministan tsaro

A wurin taron, akwai Sheikh Hussain Al Nowais, shugaban cibiyar samar da wuta ta 'Amea Power' da rukunin Otal din 'Rotana', wanda kuma ya nuna sha'awarsa ta gina Otal a Najeriya.

Sheikh Rashid Ali Rashid Lootah, shugaban kamfanin dillancin gidaje da filaye a kasar Dubai, ya shaida wa shugaba Buhari cewar kamfaninsa na da sha'awar fadada kasuwancinsa zuwa Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel