Gwamnatin Buhari ta gaza wajen magance kashe kashen yan Najeriya – Shehu Sani

Gwamnatin Buhari ta gaza wajen magance kashe kashen yan Najeriya – Shehu Sani

Sanata mai wakiltar jama’an mazabar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya bayyana gazawar shugaban kasa Muhammadu Buhari a wajen magance kashe kashen da ake samu a duk yankunan Najeriya, musamman ma jahar Zamfara.

Legit.ng ta ruwaito Shehu Sani ya bayyana haka ne a wasu bayanai daya fitar a shafinsa na Twitter, inda yace babu wata kasa a nahiyar Afirka da ake samun yawan kashe kashe kamar Najeriya.

KU KARANTA: Hattara dai: Wasu mutane na kokarin kunna wutar rikici a Kaduna

“A duk fadin Afirka babu wata kasa da ake kashe jama’a, kuma ake yin garkuwa da mutane a kullum kamar Najeriya, a gaskiya gwamnatin Najeriya ta gaza a wannan bangare na kare rayukan yan Najeriya, dole ne gwamnati ta kare rayukan yan kasa kamar yadda take kare bukatunta na siyasa.” Inji shi.

Haka zalika Sanatan ya bayyana cewa dukkanin miyagun dake aikata wannan kashe kashe sun samu makamansu ne daga wuraren yan siyasa, wadanda suka daukesu haya da nufin cimma burace buracensu na siyasa.

“Suna biyan miyagun mutane, tare da basu makamai don su taimakesu wajen cin mutuncin abokan hamayyarsu, tare da dannesu, a wasu lokuta ma har suna kashe musu duk wani dke hamayya dasu, daga baya kuma sai su raba jaha dasu, daga nan kuma sai su shiga fitinar al’umma.” Inji shi.

Haka nan Sanatan ya yi kira da gwamnati ta yi ma kowanne dan Najeriya adalci ba tare da la’akari da bambamcin addini ko kabilanci ba, da haka ne kawai za’a iya samar da zaman lafiya mai daurewa a Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel