Dakarun Sojojin Najeriya za su kaddamar da shirin 'Harbin Kunama'

Dakarun Sojojin Najeriya za su kaddamar da shirin 'Harbin Kunama'

A yau Ranar 1 ga Watan Afrilu ne Rundunar Sojojin kasa na Najeriya za su kaddamar da wani sabon shiri na musamman mai suna Ex Harbin Kunama IV domin maganin Miyagun da ke satar mutane.

Dakarun soji sun kirkiro wannan shiri ne domin kawo karshen garkuwa da jama’a da aka yi babu gaira babu dalili a irin su Jihohin Zamfara, Sokoto da kuma Katsina. Babban Jami’in sojin kasa na Najeriya Clement Abiade ya bayyana wannan.

Manjo Clement Abiade wanda shi ne Mataimakin harkokin yada labarai na sojojin Najeriya ya fadawa manema labarai wannan a Garin Sokoto. Manjo Abiade yace sojojin za su yi wannan aiki ne daga farkon Afriku har karshen watan Yuni.

KU KARANTA: Sojin sama sun dakile harin 'yan bindiga a Jihar Zamfara

Wannan aiki zai karawa jami’an tsaron kasar kwarin gwiwa don haka aka nemi jama’an da ke yankin na Sokoto da Katsina da su kwantar da hankalin su ba tare da nuna wani fargaba ba, yayin da Dakarun kasar su ka kama aiki a yau dinnan.

Rundunar sojin kasan ta Najeriya ta tabbatar da cewa babu wanda jami’an ta za su taba a wannan lokaci. Za a yi tsawon watanni 3 ana wannan aiki na Operation Harbin Kunama domin ganin an kauda Miyagu daga cikin kewayen Jihar Zamfara.

Kawo yanzu dai satar mutanen da ake yi a yankin Zamfara yayi kamari inda ake ta faman kira ga gwamnatin shugaba Buhari da ta kawowa mutanen wannan shiyya dauki domin ganin an samu tsaro.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel