Diyar Ganduje tayi kaca-kaca da masu sukar mahaifinta a Tuwita

Diyar Ganduje tayi kaca-kaca da masu sukar mahaifinta a Tuwita

Fatimah Ganduje-Ajimobi, diyar gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ta mayar da martani ga wadanda ta ce suna bata wa mahaifinta suna.

Fatima Ganduje ta zargi wasu masoya tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da nuna kamar cewa duk garin Kano babu wanda ke kaunar Ganduje.

A yayin ta ke tsokaci a kan zaben gwamna da aka gudanar a jihar Kano, Fatima Ganduje ta ce mahaifinta ya lashe zaben ne saboda yana da magoya baya sosai a kauyuka.

Sakamakon zaben ranar 9 ga watan Maris da 23 ga watan Maris ya nuna cewa Ganduje dan takarar jam'iyyar APC ya samu kuri'u 1,033,695 yayin da Abba Yusuf na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 1,024,71.

A cewar ta, mahaifinta ya raba jiha da Kwankwaso ne a lokacin da aka ce ya ci masa mutunci.

Diyar Ganduje tayi kaca-kaca da masu sukar mahaifinta a Tuwita
Diyar Ganduje tayi kaca-kaca da masu sukar mahaifinta a Tuwita
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Dattaku: Ganduje ya bayar da umurnin a mayar da hotunan Sarki Sanusi II a gidan gwamnati

"Na fito hutun cin abinci saboda haka yanzu ina da lokaci kadan, ina ku ke ne? Wasu daga cikin masu jajayen hula suna nan gidan gwamnati suna karbar shinkafa," inji ta

"Zan mayar da martani ga dukkanku saboda haka ku tsayar da jagora da zai wakilce ku. Ku natsu saboda zan muku karatun ta natsu.

"Wato abinda ya faru shine a lokacin da aka ce zabe bai kammala ba, kuna ta zagin mu amma ba mu tanka muku ba, har masu fuskoki biyu ma sun nuna kansu, yanzu kuma murna ta koma ciki mu kuma za muyi murna.

"Ba zaka zagi mahaifiyar wani kuma kayi tunanin ba za a mayar maka da martani ba. Ina da isashen data kuma idan ya kare Idris dina zai kara min.

"Kuna tunanin a Twitter ake cin zabe, mun samu kuri'u daga kauyuka saboda mu 'yan kauye ne. Dan kauye shine Gwamna.

"Kun sha kaye ne saboda Atiku bai baku kudi ba wannan karon saboda kun cuce shi a lokacin zaben shugaban kasa. Atiku bawan Allah, ina matukar ganin girmansa.

"Kuna nuna kamar cewa duk Kano babu wanda ke kaunar Ganduje, Takai na PRP wanda ya ke da kuri'u kusan 100,000 ya fadawa magoya bayansa su zabe mu ba ku ba. Kuna bakin ciki saboda munyi nasara.

"A baya muna tare da Kwankwaso kafin ya zagi kakar mu da ta rasu. Ya zo jana'izar ta a Ganduje kuma ya zage mu, a lokacin ne muka raba jiha."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel