Babu tazarce a Bauchi: PDP ta kayar da APC, INEC ta sanar da sakamon zabe

Babu tazarce a Bauchi: PDP ta kayar da APC, INEC ta sanar da sakamon zabe

Sanata Bala Mohammed, dan takarar gwamnan jihar Bauchi a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, ya lashe zaben kujerar gwamna bayan an kai ruwa rana tsakanin sa da gwamna mai ci, Mohammed Abubakar, na jam'iyyar APC.

Bayan tattara sakamako da hukumar zabe mai zaman kan ta (INEC) ta yi a yammacin ranar Litinin, an sanar da Bala Mohammed a matsayin wanda ya samu nasarar lashe kujerar gwamnan jihar Bauchi.

Dakta Musa Dahiru, sabon baturen INEC, ya ce PDP ta samu kuri'u 39,225 yayin da jam'iyyar APC ta samu kuri'u 30,055 daga sakamakon zaben raba gardama da aka yi a jihar Bauchi.

Sakamakon zaben ya hada da na karamar hukumar Tafawa Balewa da aka dade ana ta gumurzu a kan sa.

Babu tazarce a Bauchi: PDP ta kayar da APC, INEC ta sanar da sakamon zabe
Sanata Bala Mohammed
Asali: UGC

An tantance adadin ma su kada kuri'a 74,181 daga cikin mutane 139,240 da ke da katin zabe. An samu jimillar sahihan kuri'u 73,041 yayin da kuri'u 738 su ka lalace.

DUBA WANNAN: Kwankwaso da PDP ne su ka haddasa rigima lokacin zaben gwamna a Kano - BMO

Da ya ke sanar da sakamakon zaben na karshe, Dakta Dahiru ya bayyana cewar sanata Bala Muhammad ya samu jimillar kuri'u 515,113 da suka bashi nasara a kan Muhammad Abubakar, wanda ya samu kuri'u 500,622.

An cigaba da tattara sakamakon zaben ne bayan wata kotun gwamnatin tarayya dake Abuja ta ki amincewa da bukatar dakatar da INEC daga cigaba da tattara wa da sanar da sakamakon zaben da aka maimaita a jihar Bauchi. Alkalin kotun, Jastis Inyang Ekwo, ya zartar da hukuncin ne a ranar Litinin (yau).

Da yake yanke hukunci a kan zaben, Jastis Inyang, ya bayyana cewar kotu ba ta da hurumin shiga maganar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel