Siyasa: Buhari ya sha kasa, Lalong ya yi nasara a jihar Filato
Bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari, dan takara na jam'iyyar APC, ya sha mugunyar kayi yayin zaben shugaban kasa a jihar Filato, gwamnan jihar a karkashin inuwa ta jam'iyyar APC, Simon Bako Lalong, ya yi nasara bayan zaben cike gurbi da aka gudanar a ranar 23 ga watan Maris.
A yayin zaben kujerar shugaban kasa da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairun 2019, shugaban kasa Buhari ya sha babban kayi a hannun abokin adawar sa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, yayin da hukumar INEC ta bayyana sakamakon zaben jihar Filato.
Kididdigar sakamakon zaben kamar yadda hukumar INEC ta fitar ta bayyana cewa, Atiku ya lashe gamayyar kuri'u 584,665 yayin da Buhari ya samu kuri'u 468,555 a jihar Filato.
Da yake dai Hausawa na cewa sahun Keke ba ya da gaba, duk da kasancewar jam'iyya guda ta APC, Buhari ya sha kayi a jihar Filato yayin da Gwamna Lalong ya yi nasara ta samun tazarce a kujerar sa.
Hukumar INEC ta bayyana cewa, yayin da Gwamna Lalong ya yi nasar da gamayyar kuri'u 595,582, abokin adawar sa na jam'iyyar PDP, Janar Jerimiah Useni, ya samu kuri'u 546,813 kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito.
KARANTA KUMA: Gwamna Lalong ya yi murna ta samun nasarar tazarce
Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya sha kyar wajen lashe zaben kujerar gwamnan jihar sa yayin zaben cike gurbi da hukumar INEC ta gudanar a ranar Asabar.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng