Da duminsa: 'Yan bindiga sunyi awon gaba da basarake a jihar Edo

Da duminsa: 'Yan bindiga sunyi awon gaba da basarake a jihar Edo

Rahoton da Legit.ng ta samu na nuni da cewa wasu 'yan bindiga da ba san ko su wanene ba sun sace basarake Enogie of Ukiri a karamar hukumar Ikpoba-Okha na jihar Edo mai suna Godwin Aigbe.

Punch ta ruwaito cewa wasu maza dauke da makamai wanda adadin su ya kai biyar ne su kayi kutse cikin fadar basaraken a sanyin safiyar ranar Asabar.

An ce sun ta harbe-harben harsashi a iska kafin su kayi awon gaba da Enogie zuwa wani wuri da ba a sani ba.

DUBA WANNAN: Da duminsa: CP Singham Wakili ya taimaki PDP tayi mana magudi a Kano - APC

'Yan bindiga sunyi awon gaba da basarake a jihar Edo
'Yan bindiga sunyi awon gaba da basarake a jihar Edo
Asali: Twitter

Wata majiya daga kauyen ta ce 'yan bindigan sun bankawa motarsu wuta kafin suka tasa keyar basaraken cikin motarsa kirar Nissan Sunny suka tafi da shi.

An gano cewar sun kama hanyar jihar Delta da basaraken.

Enogie dai tsohon sufritandan 'yan sanda ne da ya gaji mahaifinsa da ya rasu wasu shekaru da suka gabata.

Kakakin yan sandan na jihar, Chidi Nwabuzor ya tabbatar da afkuwar lamarin a hirar ya yi da majiyar Legit.ng inda ya ce tuni sun fara bincike a kan lamarin.

"Eh, da gaske ne, Yan sanda sun fara bincike a kan lamarin domin tabbatar da cewa an kwato basaraken cikin koshin lafiya," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel