Rikicin Jalingo: Anyi musayar kalamai tsakanin APC da gwamnatin Taraba

Rikicin Jalingo: Anyi musayar kalamai tsakanin APC da gwamnatin Taraba

Gwamnatin jihar Taraba karkashin jagorancin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tana musayar kalamai tsakanin ta da jam'iyyar adawa ta All Progressives Congress (APC) a kan rikicin da ya faru a Jalingo, babban birnin jihar.

Gwamnatin jihar tayi ikirarin cewa magoya bayan jam'iyyar APC ne suka fara kai harin da ya yi sanadiyar barkewar rikicin amma jam'iyyar ta APC sun mayar da martani inda su kayi ikirarin cewa PDP da gwamnatin jihar Taraba ne suka hada kai suka kaiwa magoya bayan jam'iyyar APC hari.

Kwamishin watsa labarai na jihar, Mr Simon Dogari ya yi ikirarin cewa wadanda suka sha kaye a zaben jihar ne suka dauki nauyin 'yan daba domin tayar da rikici a babban birnin jihar a yayin da ya ke yiwa manema labarai jawabi.

DUBA WANNAN: Da duminsa: CP Singham Wakili ya taimaki PDP tayi mana magudi a Kano - APC

Rikicin Jalingo: Anyi musayar kalamai tsakanin APC ga gwamnatin Taraba
Rikicin Jalingo: Anyi musayar kalamai tsakanin APC ga gwamnatin Taraba
Asali: Twitter

Dogari ya yi ikirarin cewa wadanda suka sha kaye a zaben sun tayar da rikicin ne domin suna son kawo cikas ga zaben gwamna da aka gudanar a jihar cikin zaman lafiya da aminci.

Sai dai, shugaban jam'iyyar APC na jihar, Barrister Ibrahim El-Sudi ya karyata wannan zargin inda ya ce gwamnatin jihar da jam'iyyar PDP ne suka shirya harin.

El-Sudi ya ce suna da cikakken bayani a kan dukkan barnar da jam'iyyar PDP da gwamnatin jihar suka rika aikatawa.

Shugaban na APC da ya ce har yanzu ana kaiwa magoya bayan jam'iyyarsu hari a wurare daban-daban na jihar ya yi kira da su zauna lafiya kuma su guji daukan doka a hannunsu. Ya ce APC za ta kalluballanci sakamakon zaben a kotu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel