Mawakin Abba Gida-Gida ya jagoranci mawaka da 'yan fim yin zanga-zanga a Kano, hotuna

Mawakin Abba Gida-Gida ya jagoranci mawaka da 'yan fim yin zanga-zanga a Kano, hotuna

A yau, Alhamis, ne Tijjani Gandu, mawakin da ya rera wakar ‘Abba gida-gida’ ga Abba Kabir Yusuf, dan takarar kujerar gwamnan jihar Kano a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, ya jagoranci ragowar wasu mawaka da ‘yan fim wajen gudanar da zanga-zanga a kan sakamakon zaben gwamna a jihar Kano.

Mawakin tare da abokansa sun gudanar da zanga-zangar ne domin nuna rashin amincewar sa da matakin hukumar zabe ta kasa (INEC) ta dauka na bayyana cewar zaben ‘bai kammalu ba’ duk da kasancewar dan Abba ne ke kan gaba wajen yawan kuri’u.

Mawakin Abba Gida-Gida ya jagoranci mawaka da 'yan fim yin zanga-zanga a Kano, hotuna
Mawaka da 'yan fim sun yi zanga-zanga a Kano
Asali: Facebook

Mawakin Abba Gida-Gida ya jagoranci mawaka da 'yan fim yin zanga-zanga a Kano, hotuna
Mawakin Abba Gida-Gida ya jagoranci mawaka da 'yan fim yin zanga-zanga a Kano
Asali: Facebook

Mawakin Abba Gida-Gida ya jagoranci mawaka da 'yan fim yin zanga-zanga a Kano, hotuna
Mawaka da 'yan fim yin zanga-zanga a Kano
Asali: Facebook

Mawakin Abba Gida-Gida ya jagoranci mawaka da 'yan fim yin zanga-zanga a Kano, hotuna
Mawakin Abba Gida-Gida; Tijjani Gandu

Alan waka
Asali: Facebook

Mawakin Abba Gida-Gida ya jagoranci mawaka da 'yan fim yin zanga-zanga a Kano, hotuna
Mawaka da 'yan fim yin zanga-zanga a Kano
Asali: Facebook

Zanga-zangar mawakan na zuwa ne a daidai lokacin da Salihu Tanko Yakasai, mai taimaka wa gwamnana jihar Kano a bangaren kafafen sadarwa na zamani, ya karyata wani faifan bidiyo da ke yawo a dandalin sada zumunta a kan cewar wasu matasa da ke goyon bayan Kwankwasiyya sun kutsa cikin gwamnatin Kano tare da korar gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

DUBA WANNAN: Manufar maimaita zabe a wajen ‘yan takarar jam’iyyar APC – Sanata Shehu Sani

A wani sako da ya fitar a tare da hoton gidan gwamnatin jihar Kano shafinsa na Tuwita (@dawisu), Yakasai ya ce, “wannan shine gidan gwamnatin jihar Kano, haka ginin gidan ya ke tun lokacin mulkin mallaka duk da a kan yi ma sa kwaskwarima lokaci zuwa lokaci. Duk wani wanda ya ce ‘yan daba sun bankara sun shiga gidan karya ya ke, kuma kun san su waye ma su yada irin wannan irin wannan karyar."

Hadimin gwamnan ya bayyana cewar faifan bidiyon an nade shi a taron da Kwankwaso ke yi da ‘yan dabar sa a gidan sa.

Yakasai ya kara da cewa mabiya Kwankwasiyya ne su ka fara kirkirar labarin tare da yada shi duk da sun san babu gaskiya a cikin sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel