‘Yan Kwankwasiyya ba su kori Ganduje daga gidan gwamnati ba – Hadimin Ganduje

‘Yan Kwankwasiyya ba su kori Ganduje daga gidan gwamnati ba – Hadimin Ganduje

Salihu Tanko Yakasai, mai taimaka wa gwamnana jihar Kano a bangaren kafafen sadarwa na zamani, ya karyata wani faifan bidiyo da ke yawo a dandalin sada zumunta a kan cewar wasu matasa da ke goyon bayan Kwankwasiyya sun kutsa cikin gwamnatin Kano tare da korar gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

A wani sako da ya fitar a tare da hoton gidan gwamnatin jihar Kano shafinsa na Tuwita (@dawisu), Yakasai ya ce, “wannan shine gidan gwamnatin jihar Kano, haka ginin gidan ya ke tun lokacin mulkin mallaka duk da a kan yi ma sa kwaskwarima lokaci zuwa lokaci. Duk wani wanda ya ce ‘yan daba sun bankara sun shiga gidan karya ya ke, kuma kun san su waye ma su yada irin wannan irin wannan karyar."

Hadimin gwamnan ya bayyana cewar faifan bidiyon an nade shi a taron da Kwankwaso ke yi da ‘yan dabar sa a gidan sa.

Yakasai ya kara da cewa mabiya Kwankwasiyya ne su ka fara kirkirar labarin tare da yada shi duk da sun san babu gaskiya a cikin sa.

Kazalika, Yakasai ya bayyana cewar wannan ba shine karo na farko da mabiya su ka kirkiri tare da yada labaran karya a kan gwamna Ganduje.

‘Yan Kwankwasiyya ba su kori Ganduje daga gidan gwamnati ba – Hadimin Ganduje
Gidan gwamnatin jihar Kano
Asali: Twitter

Ya ce ko a ranar Lahadi haka ‘yan Kwankwasiyya su ka kirkiri wani labarin karya da ke nuna cewar gwamnan jihar Kaduna ya shigo Kano domin taimakon Ganduje a kan zaben kujerar gwamnan jihar Kano da aka yi ranar Asabar, 9 ga watan Maris.

DUBA WANNAN: Sakamakon zabe: hadimin Ganduje ya yi murabus saboda Abba Gida-Gida

Al’amuran siyasa na kara daukan zafi a jihar Kano tun bayan da hukumar zabe ta kara (INEC) ta bayyana zaben kujerar gwamnan jihar a matsayin ‘bai kammalu’ ba saboda yawan kuri’un da aka soke yayin zabe sun fi banbancin da ke tsakanin dan takarar jam’iyyar PDP< Abba Kabir Yusuf, da gwamna mai ci, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel