Wata sabuwa: Budurwa ta kai karar mahaifinta gaban kotu akan auren dole

Wata sabuwa: Budurwa ta kai karar mahaifinta gaban kotu akan auren dole

Wata buduwar mai suna Aisha Isah ta shigar da karar mahaifinta Malam Isah Ibrahim gaban wata kotun shari’ar Musulunci dake zamanta a unguwar Magajin Gari dake jahar Kaduna, akan kokarinsa na daura mata auren dole tare da garkameta a cikin gida.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Aisha, wanda take zaune a unguwar Kadaure ta shaida ma kotun cewa mahaifinta ya matsa mata akan tayi aure, har ma yana mata barazanar auren dole, amma saboda taki amincewa da auren, shine ya garkameta a cikin gida, babu shiga babu fita.

KU KARANTA: Jama’an Ganduje da na Abba gida gida sun gudanar da addu’o’in samun nasara a zaben Kano

Don haka Aisha ta nemi kotun data tilasta ma mahaifinta saketa daga gidan daya garkameta, haka nan ta nemi kotun ta ja hankalinsa daya daina yi mata barazanar auren dole, har sai lokacin da ta samun mijin da take so da aure.

Sai dai mahaifin Aisha, Malam Isah Ibrahim ya musanta wannan zarge zarge na diyarsa, inda ya bayyana ma kotun cewa shi fa ya nemi Aisha ta zabi mijin da take so daga cikin dimbin samarin dake auwa wajenta ne, don yayi mata aure.

“Mutane da dama sun bayyana min yadda diyata take kawo mazaje daban daban gudana, wannan ne yasa na garkameta a cikin gida domin babu wani uban kirki da zai yarda da abinda take yi.” Inji shi.

Bayan sauraron dukkanin bangarorin biyu, Alkalin kotun, Mai sharia Malam Dahiru Lawal Abubakar ya nemi Aisha da ta yi sulhu da mahaifinta, kuma ta guji aikata duk wasu abubuwa da zasu iya zama cin fuska ga iyayenta.

Sa’annan ya shawarci Uban Aisha, Malam Isah daya yi hakuri da diyarsa, kuma ya bi hanyoyin da shari’ar Musulunci ta zayyana wajen aurar da diya mace, daga karshe kuma ya dage sauraron karar zuwa ranar 20 ga watan Maris.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel