An fitar da Miliyan 230 daga akawun din Gwamnatin Kano da za a raba a Kananan hukumomi

An fitar da Miliyan 230 daga akawun din Gwamnatin Kano da za a raba a Kananan hukumomi

Mun samu labari cewa gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya cire wasu makudan kudi har Naira miliyan 233.5 da ake zargin cewa za ayi amfani da su ne wajen sayen kuri’a a zaben da za a karasa nan gaba.

An fitar da Miliyan 230 daga akawun din Gwamnatin Kano da za a raba a Kananan hukumomi
Gwamnatin Kano ta cire Miliyan 230 daga asusun ta a makon nan
Asali: Facebook

Wasu takardu da su ka shigo hannun jaridar Daily Nigerian sun tabbatar da Gwamnatin Kano ta zare kudi har sama da Naira Miliyan 230 asusun jihar a Ranar Talata bayan an sanar da cewa ba a kammala zaben jihar ba.

A wata wasika da ta fito daga hannun Ma’aikatar kananan hukumomi, gwamnatin Kano ta cire kudi daga bankin Unity Bank inda aka zargin cewa za a batar da kudin nan ne a wuraren da za a sake zaben gwamna a Kano.

KU KARANTA: Wani kwara da ke aiki a Jihar Kano ya fada hannun ‘Yan bindiga

An fitar da Miliyan 230 daga akawun din Gwamnatin Kano da za a raba a Kananan hukumomi
Yadda Ganduje ya shirya batar da Miliyan 230 a wasu Kananan hukumomi
Asali: Twitter

Majiyar ta bayyana cewa ta-ka-nas aka cire wadannan makudan miliyoyi domin ayi amfani da su wajen sayen kuri’ar mutanen da ke cikin kananan hukumomi 22 da za a kammala zaben gwamna a Ranar 23 ga Watan nan.

A wannan takarda, an yi bayani dalla-dalla na inda za a kashe wadannan kudi. Karamar hukumar Kabo, inda daga nan Murtala Sule Garo ya fito ne za a fi kashe kudin. Garo shi ne kwamishina na kananan hukumomin jihar.

Jaridar tace ta nemi Murtala Garo yayi magana game da wannan batu amma yayi gum. Yanzu haka dai ana ta kama ‘yan jam’iyyar APC su na kokarin sayen katin zaben mutane a cikin Garin na Kano.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel