Ku sanar da sakamakon zaben jihar Kano - PDP ta gargadi INEC
Jam'iyyar PDP a Kano ta yi kira ga hukumar zabe ta kasa (INEC) da ta bayyana sakamakon zaben kujerar gwamnan jihar da aka gudanar ranar Asabar muddin ana bukatar zaman lafiya a jihar.
Shugaban jam'iyyar PDP a jihar Kano, Dakta Rabi'u Suleiman Bichi, ne ya yi wannan gargadi da safiyar yau, Litinin, a hedikwatar hukumar zabe ta Kano.
A cewar Bichi; "a bayyane ta ke bayan tattara sakamakon kananan hukumomi 43 cewar jam'iyyar PDP ce gaba amma don abun kunya sai wasu 'yan daba su ka yi kutse cibiyar tattara sakamako ta karamar hukumar Nasarawa su ka yaga takardun sakamakon zabe.
"Mu na kira ga INEC da ta bayyana sakamakon nasarar da jam'iyyar PDP ta samu idan ya so daga baya su tattara ragowar sakamakon.
"Yin hakan ne kadai zai haifar da zaman lafiya a jihar Kano, sabanin haka kuma zai iya haifar da wani abu daban. Idan har zaman lafiya ake so, INEC ta bayyana PDP a matsayin jam'iyyar da ta lashe zabe a jihar Kano."
Labarin da Legit.ng Hausa ta samu daga wata majiya mai tushe daga Kano na nuni da cewar rundunar 'yan sanda karkashin jagorancin kwamishina CP Muhammad Wakili ta saki mataimakin gwamnan jihar, Nasiru Yusuf Gawuna, da kwamishinan kananan hukumomi, Nasiru Sule Garo.
Rundunar 'yan sanda ta kama manyan jami'an gwamnati biyu ne a daren jiya bayan sun yi kutse tare da kawo hayaniya a cibiyar tattara sakamakon zaben gwamna a karamar hukumar Nassarawa.
DUBA WANNAN: APC ta lashe kujeru 30 na majalisar dokokin jihar Jigawa
Ana zargin mataimakin gwamnan da kwamishinan da yaga takardun sakamakon karamar hukumar Nasarawa da ake jira domin kammala tattara sakamakon zaben kujerar gwamna a matakin jiha.
Jihar Kano na da kananan hukumomi 44 kuma tuni sakamako daga kananan hukumomi 43 sun shiga hannun baturen zabe na jihar in banda karamar hukumar Nasarawa.
Jam'iyyar PDP ce a gaba a sakamakon kananan hukumomi 43 da su ka shigo hannu, sai dai babu tazara mai yawa tsakanin ta da jam'iyyar APC.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng