Siyasar Kano: Doguwa da Mutanen sa sun sauya-sheka zuwa APC

Siyasar Kano: Doguwa da Mutanen sa sun sauya-sheka zuwa APC

Yayin da ake shiryawa zaben gwamnonin jihohi a Najeriya, mun ji labari cewa shugaban bangaren jam’iyyar adawa na PDP a jihar Kano Sanata Mas’ud Doguwa da majalisar sa sun sauya-sheka zuwa APC.

Siyasar Kano: Doguwa da Mutanen sa sun sauya-sheka zuwa APC
Wasu manyan PDP sun fice zuwa APC ana shirin zaben Gwamnoni
Asali: Facebook

Mun ji cewa dinbin magoya bayan jam’iyyar ta PDP sun fice zuwa APC mai mulki a jihar Kano bayan da manyan Jagororin Jam’iyyar ta PDP sun sauya-sheka zuwa APC yayin da ake daf da a gudanar da zaben gwamnonin jihohi.

Daily Nigerian ta rahoto mana labari cewa sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na ‘yan taware a Kano, Musa Danbirni, ya tabbatar da cewa mutum 12 cikin 14 na shugabannin PDP na jihar sun koma cikin tafiyar APC.

KU KARANTA: Wadanda ke neman kujerar Ganduje sun gana da Kwankwaso

Musa Danbirni ya bayyana cewa taron mabiyan su sun koma bayan gwamna Abdullahi Umar Ganduje, inda za su taya sa yakin neman zabe. An samu baraka ne tun bayan da PDP ta soke shugabancin jihar kwanakin baya.

Kafin nan wasu manyan PDP irin su Imam Buhari, Ahmed Salik da Surajo Marshall sun bar PDP zuwa APC. Haka kuma rikakkun ‘yan siyasa irin su Yahaya Bagobiri, sun nuna goyon bayan su gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje.

Dazu nan mu ka ji labari cewa kotu ta dakatar da ‘dan takarar gwamnan Kano na PDP, Injiniya Abba Kabir Yusuf, daga tsayawa takara bayan Ibrahim Little ya shigar da kara gaban Alkali kwanaki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel