Nasarar Buhari ta tayar da tarzoma a garin Legas, Oyo, Abuja

Nasarar Buhari ta tayar da tarzoma a garin Legas, Oyo, Abuja

Bayar da sanarwa ta nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin zakara wanda ya lashe babban zaben kasa da aka gudanar a ranar Asabar ta makon da ya gabata, ya janyo wani mummunan hargisti da ya yi sanadiyar salwantar rayuka cikin jihar Legas.

Da sanadin shafin jaridar Vanguard mun samu cewa, rayukan mutane uku sun salwanta yayin barkewar wani mummunan hargitsi a yankin Okokomaiko da Lagos Island da ke jihar Legas biyo bayan sanarwa ta nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Rayukan wani jami'in hukumar 'yan sanda da kuma wasu 'yan Tireda biyu sun salwanta inda a halin yanzu wani jami'i ke ci gaba da jinya a gadon asibiti bayan da masu ta'ada suka kai farmaki yankin Alaba Rago da ke jihar Legas.

Nasarar Buhari ta tayar da tarzoma a garin Legas, Oyo, Abuja
Nasarar Buhari ta tayar da tarzoma a garin Legas, Oyo, Abuja
Asali: UGC

Mutane da dama sun samu munanan raunuka daban-daban yayin aukuwar wannan mummunan hargitsi da murna gami da farin ciki ta nasarar shugaban kasa Buhari ta haifar kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito.

Rahotanni kamar yadda shafin jaridar Vanguard ya ruwaito sun bayyana cewa, lamarin ya auku ne biyo bayan wasu gungun Matasan Hausawa da suka aiwatar da yawan shawagi na bayyana farin ciki kwararo-kwararo tare da wake mai amso ta Sai Baba a yankunan unguwar Okokomaiko.

Al'ummar yankin Lugbe daura da hanyar filin jirgin sama da ke babban birnin tarayya na Abuja, sun shiga cikin rudani yayin da magoya bayan shugaban kasa Buhari dauke da miyagun makamai suka datse-datse hanyoyi domin bayyana farin cikin samun nasarar sa.

KARANTA KUMA: Sakamakon Zabe: PDP na shirin tayar da bore a Najeriya

A can birnin Ibadan na jihar Oyo, an ci zarafin al'umma inda wata 'yar tireda da ta bukaci a sakaya sunan ta ta yi koken yadda magoyan shugaba Buhari da jam'iyyar APC suka haramta masu gudanar da harkokin kasuwanci.

Yayin kira ga gwamnan jihar Abiola Ajimobi da kuma hukumomin tsaro, wannan Mata ta shaidawa manema labarai yadda magoya baya na jam'iyyar APC suka shimfida masu sharadin ci gaba da gudanar da harkokin su na kasuwanci da cewar tilas sai sun zabi jam'iyyar APC yayin zaben gwamna da za a gudanar a ranar 9 ga watan Maris, 2019.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel