Fiye da mutum miliyan 8 ma su katin zabe INEC ta hana kada kuri’a – Peter Obi

Fiye da mutum miliyan 8 ma su katin zabe INEC ta hana kada kuri’a – Peter Obi

Peter Obi, dan takarar neman mataimakin shugaban kasar Najeriya a karkashin inuwar PDP, ya yi zargin cewar an yi ba daidai ba a zaben shugaban kasa da aka gudanar ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu.

Obi ya zargi hukumar zabe ta kasa (INEC) da hana ‘fiye da mutum miliyan 8’ da ke da katin zabe a yankin kudu ma so gabas su kada kuri’a, ya na mai bayyana cewar kaso 20 ne kawai na ma su katin zabe su ka kada kuri’a a yankin.

Da ya ke Magana da ‘yan jarida a jiya, Talata, a gidan sa da ke garin Onitsa, Obi ya yi zargin cewar an yi amfani da wani salon magudi domin ganin cewar ma su katin zabe a yankin ba su samu damar kada kuri’a ba.

Sannan ya nuna shakku a kan sakamakon zaben shugaban kasa daga jihohin Yobe da Borno da shugaba Buhari ya samu kuri’u ma su yawa duk da su na fama da rikicin Boko Haram.

Fiye da mutum miliyan 8 ma su katin zabe INEC ta hana kada kuri’a – Peter Obi
Peter Obi yayin kada kuri'a
Asali: UGC

Idan ba ku manta ba tun a ranar zabe na bayyana cewa akwai almundahana a cikin harkar bayan samun rahoton cewar jama’a da dama ba su samu damar kada kuri’a ba saboda matsalar na’urar tantance ma su zabe,” a cewar sa.

Sannan ya cigaba da cewa “tun a lokacin da na samu labarin cewar na’urar tantance ma su zabe guda 400,000 sun kone amma INEC ba ta yi komai a kai ba na san cewar akwai makarkashiya, saboda ba za su bari jama’a su kada kuri’a ba tare da na’uara ta tantance su ba.

DUBA WANNAN: Ka yi koyi da Jonatahan – Jigo a PDP ya bawa Atiku shawara

“Amma a wani bangaren na kasar nan sun bar jama’a sun yi zabe ba tare da na’ura ta tantance su ba kuma an yi amfani da sakamakon zaben a haka.

Ya za a ce jihohi kamar Yobe da Borno sun samar da kuri’u fiye da na jihohin Anambra da Ebonyi? Jihohin biyu sun dade a cikin yanayin yaki amma duk da haka na’urori ba su bayar da matsala a jihohin ba.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel