Yadda Buhari ya yi murdiyya wajen lashe zaben 2019 - Sheikh Ahmad Gumi

Yadda Buhari ya yi murdiyya wajen lashe zaben 2019 - Sheikh Ahmad Gumi

Babban Malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana soki Shugaba Muhamadu Buhari bisa nasarar da ya samu na lashe zaben shugabancin kasa na 2019 da aka gudanar a ranar 23 ga watan Satumba kuma aka sanar da sakamakon zaben a ranar 27 ga watan Fabrairu.

Sheikh Gumi ya koka kan yadda Buhari ya yi gadarar cewa shine zai lashe zaben tun kafin a fara kirga kuri'u da al'umma suka kada.

Yadda Buhari ya yi murdiyya wajen lashe zaben 2019 - Dr Gumi
Yadda Buhari ya yi murdiyya wajen lashe zaben 2019 - Dr Gumi
Asali: Twitter

Kamar yadda muka samu daga Daily Nigerian, Sheikh Gumi ya ce, "Tun kafin a kirga kuri'u, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi imani 100% cewa shine zai lashe zabe. Ta yaya ya san shine zai lashe zaben duba da cewa kan 'yan kasar a rabe ta ke kuma ana fama da talauci da fatara?

DUBA WANNAN: Cin zaben APC: Dubban al'umma sun mamaye titunan Sokoto

"Ba dai zai ce ayyukansa da cancantarsa bane suka sanya shi ya lashe zabe. Tattalin arziki, tsaro da rashawa duk sunyi katutu a kasar. Kasar na fama da karancin ayyukan yi, ana samun karuwar kashe-kashe na kabilu, ana samun karuwar sace mutane, talauci da rashawa a ko wane lungu da sako.

"Abinda kawai zai sanya shi ya bugi kirji ya ce shine zai lashe zabe itace karfin mulki da ya ke dashi a matsayinsa na shugaba wanda shi ake nufi da halastaciyar rashawa.

"Duba TraderMoni da aka kaddamar watanni kadan kafin zabe sannan ana amfani da EFCC wurin musguwanawa abokan hammaya, amfani da kudin gwamnati wurin shirya kamfe, mamaye gidajen talabijin da rediyo na gwamnati da kuma amfani da masallatai domin yin kamfen da amfani da sojoji domin razana masu zabe da sauransu, halastaciyar rashawar na da yawa."

Sheikh Gumi ya koka kan yadda jam'iyyar APC ta rika rabawa mata a kauyuka N500 domin su zabi APC tare da amfani yara wanda shekarunsu bai kai na zabe ba wurin kada kuri'a da kuma yim amfani da mimbarin malamai domin kamfe.

Babban malamin ya yadawa dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar saboda jajircewarsa. Ya kuma shawarce shi ya yi watsi da sakamakon zaben ya garzaya kotu domin a bi masa hakkinsa kamar yadda Shugaba Buhari ya yi a baya.

Ya kuma yi kira ga al'umma su cigaba da zama lafiya tare da biyaya ga doka da oda.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel