Sakamakon zabe: Hadimin El-Rufai ya yi ma Shehu Sani rubdugu a zaben Sanata

Sakamakon zabe: Hadimin El-Rufai ya yi ma Shehu Sani rubdugu a zaben Sanata

Tun bayan kammala kada kuri’u a babban zaben Najeriya daya gudana a ranar Asabar, 23 ga watan Feburairu ne aka fara tattara alkalumman sakamakon zaben daga kowace rumfa, mazaba, karamar hukuma, jaha da ma kasa baki daya, tare da kidayarsu.

Kuma zuwa yanzu an fara samun tabbatattu kuma sahihan sakamakon zabukan da suka gudana, inda yan siyasa da dama da suka tsaya takara sun fara sanin matsayinsu, walau sun samu nasara ko kuma akasin haka, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

KU KARANTA: Sakamakon zabe: Wasu gwamnonin 2 da suka tunkuyi kasa a zaben Sanatoci

Sakamakon zabe: Hadimin El-Rufai ya yi ma Shehu Sani rubdugu a zaben Sanata
Shehu da Uba
Asali: UGC

Haka labarin yake a jahar Kaduna, inda zuwa yanzu Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya san matsayinsa bayan tsohon abokinsa, kuma amininsa, mai baiwa gwamnan jahar Kaduna shawara akan harkar siyasa, Uba Sani ya tikashi da kasa.

Uba Sani na jam’iyyar APC ya samu nasara ne da kuri’u 355,242, yayin da dan takarar jam’iyyar PDP, Lawal Adamu Mista LA yake da kuri’u 195,497, sai Sanata Shehu Sani na PRP daya samu kuri’u 70,613, da wannan a iya cewa Shehu Sani ya shirya barin gado don baiwa tsohon abokinsa dama ya hau.

Ba wani bane ya tabbatar da ingancin wannan sakamako daya wuce baturen zaben mazabar Kaduna ta tsakiya, Farfesa Zakari Muhammad na jami’ar Ahmadu Bello, kamar yadda ya sanar a ranar Talata a garin Kaduna.

Ga masu bibiyan al’amuran siyasar jahar Kaduna sun sani cewa a shekarar 2015 ne Sanata Shehu Sani ya dare kujerar Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa bayan ya lashe zabe a inuwar APC, sai dai zama bai yi dadi tsakaninsa da Gwamna El-Rufai ba, don haka ya sauya sheka zuwa PRP.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel