Sakamakon zabe: Tsofaffin gwamnonin Najeriya 7 da suka lashe zaben Sanata

Sakamakon zabe: Tsofaffin gwamnonin Najeriya 7 da suka lashe zaben Sanata

Tun bayan kammala kada kuri’u a babban zabenkasar Najeriya daya gudana a ranar Asabar, 23 ga watan Feburairu ne aka fara tattara alkalumman sakamakon zaben daga kowace rumfa, mazaba, karamar hukuma, jaha da ma kasa baki daya, tare da kidayarsu.

Sai dai zuwa yanzu an fara samun tabbatattu kuma sahihan sakamakon zabukan da suka gudana, inda yan siyasa da dama da suka tsaya takara sun san matsayinsu, walau sun samu nasara ko kuma akasin haka.

KU KARANTA: Dan hakin daka raina: Jam’iyyar PRP ta bada mamaki a jahar Bauchi

Da wannan ne Legit.ng ta tattaro muku alkalumman wasu tsofaffin gwamnonin Najeriya da suka samu nasarar lashe zaben takarar Sanata a yankunansu, wanda hakan ke nufin za’a cigaba da jin amonsu kenan a farfajiyar siyasar Najeriya.

Tsohon gwamnan jahar Kano Malam Ibrahim Shekarau zai shiga majalisar dattawa a matsayin Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya a karo na farko, inda ya kujerar daga hannun Kwankwaso bayan ya samu nasara a zaben ranar Asabar.

Shekarau na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 506, 271, yayin da dan takarar jam’iyyar PDP kuma dan Kwankwasiyya, Aliyu Sani Madakin gini ya samu kuri’u 276, 768, kamar yadda baturen zabe Farfesa Adamu Alhaji Sama’ila ya bayyana.

Shima tsohon gwamnan jahar Abia, Orji Uzor Kalu ya lashe Sanatan Abia ta tsakiya a karkashin inuwar jam’iyyar APC da kuri’u 31, 203, inda ya kada Sanata mai ci na jam’iyyar PDP, Mao Ohuabunwa daya samu kuri’u 20, 801.

Sanata Aliyu Magatakardan Wammako, tsohon gwamnan jahar Sakkwato ma ya samu nasarar komawa kujerarsa a inuwar jam’iyyar APC bayan ya lashe zaben da kuri’u 172,980, yayin dan takarar PDP, Ahmed Muhammad Maccido ya samu kuri’u 138,922.

Sai kuma tsohon gwamnan jahar Enugu, Chimaroke Nnamni, wanda ya lashe zaben Sanatan mazabar Enugu ta gabas a karkashin inuwar jam’iyyar PDP da kuri’u 128, 843, yayin da abokin hamayyarsa na APGA, Uchenna Agbo ya samu kuri’u 14,225.

Akwai Abdullahi Adamu, tsohon gwamnan jahar Nasarawa, wanda shima ya samu nasarar lashe zaben Sanatan mazabar Nassarawa ta yamma a inuwar jam’iyyar APC da kuri’u 115,298, yayin da dan takarar PDP, Bala Ahmed Aliyu ya samu 85,615.

Shima tsohon gwamnan jahar Kebbi, Sanata Adamu Aliero ya samu nasarar sake komawa majalisar dattawa a inuwar jam’iyyar APC bayan ya lashe zabe kuri’u 232,000, inda ya buge abokin takararsa daga PDP, Shehu Abubakar daya samu kuri’u 75,638.

Sanata Danjuma Gobe, tsohon gwamnan jahar Gombe ma ya lashe zaben Sanatan Gombe ta tsakiya, a wannan karo ya samu kuri’u 110,116, wanda ya doke dan takarar jam’iyyar PDP Abubakar Nono mai kuri’u 39,760.

Ba za’a rasa wasu tsofaffin gwamnonin da suka fafata a zaben Sanata a wasu jihohin Najeriya ba, amma dai zuwa yanzu wadannan da muka ambata sune wadanda aka sanar da nasararsu a hukumance.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel