Zaben 2019: Buhari ya tumurmusa Atiku a jihar Kano
A yayin da tiryan-tiryan sakamakon babban zaben kasa da aka gudanar a ranar Asabar ke ci gaba da bayyana, mun samu cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yiwa Atiku Abubakar diban Karan Mahaukaciya a jihar Kano.
KARANTA KUMA: Sakamakon zabe daga jihohin Kano, Adamawa, Yobe da Borno
Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari da ya kasance dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar APC, ya yiwa abokin adawar na jam'iyyar PDP, Atiku, bugun dawa yayin da hukumar zabe ta kasa ta kammala kididdiga da kidayar sakamakon zaben jihar Kano.
Shafin jaridar Sahara Reporters ya ruwaito cewa, Shugaban kasa Buhari ya yi nasara cikin dukkanin kananan hukumomi 44 na jihar Kano yayin da Atiku ya tashin fam-fam-fam ba tare da samun nasara a ko guda ba.
Rahotanni sun bayyana cewa, Buhari ya kare martabar mahaifar sa ta jihar Katsina inda ya lallasa Atiku da fifikon kuri'u 900,000. Kazalika Atiku ya kare martabar mahaifar sa ta jihar Adamawa, inda ya yiwa Buhari shigar wuri da kimanin kuri'u 410,266.
Dalla-Dalla ga yadda sakamakon zaben jihar Kano tsakanin Buhari da Atiku ya kaya kamar yadda hukumar zabe ta kasa wato INEC ta wassafa:
1. Garun Mallam LGA
APC: 23,810
PDP: 4,861
2. Tofa LGA
APC: 19,984
PDP: 7,732
3. Kunchi LGA
APC:20,375
PDP: 4,983
4. Bagwai LGA
APC: 23,375
PDP: 10,584
5. Gabasawa LGA
APC: 24,420
PDP: 6,130
6. Bunkure LGA
APC: 27,232
PDP: 9,528
7. Rimin Gado LGA
APC: 20,589
PDP: 10,305
8. Karaye LGA
APC: 23,023
PDP: 8,265
9. Madobi LGA
APC: 26,110
PDP: 13,113
10. Dawakin Tofa LGA
APC: 37,417
PDP: 6,507
11. Tudun Wada LGA
APC: 38,865
PDP: 10,707
12. Tsanyawa LGA
APC: 25,823
PDP: 5,399
13. Sumaila LGA
APC: 34,609
PDP: 4,904
14. Gwarzo LGA
APC: 33,581
PDP: 10,682
15. Kibiya LGA
APC: 18,085
PDP: 11,028
16. Rano LGA
APC: 23,855
PDP: 7,055
17. Agingi LGA
APC: 21,458
PDP: 5,267
18. Gezawa LGA
APC: 29,954
PDP: 8,246
19. Gwale LGA
APC: 50,834
PDP: 12,283
20. Bebeji LGA
APC: 26,023
PDP: 8,190
21. Gaya LGA
APC: 25,864
PDP: 6,577
22. Albasu LGA
APC: 26,412
PDP: 10,285
23. Warawa LGA
APC: 19,073
PDP: 6,101
24. Ungogo LGA
APC: 51,842
PDP: 10,475
25. Minjibir LGA
APC: 27,725
PDP: 5,870
26. Garko LGA
APC: 22,356
PDP: 2,840
27. Doguwa LGA
APC: 25,454
PDP: 7,013
28. Kabo LGA
APC: 29,482
PDP: 8,955
29. Kiru LGA
APC: 36,739
PDP: 12,205
30. Shanono LGA
APC: 24,173
PDP: 8,469
31. Dambatta LGA
APC: 31,850
PDP: 6,947
32. Wudil LGA
APC: 28,755
PDP: 5,108
33. Bichi LGA
APC: 42,714
PDP: 11,050
34. Dawakin Kudu LGA
APC: 39,261
PDP: 10,751
35. Kura LGA
APC: 34,996
PDP: 9,047
36. Kumbotso LGA
APC: 53,923
PDP: 11,366
37. Takai LGA
APC: 38,477
PDP: 5,877
38. Makoda LGA
APC: 24,749
PDP: 3,234
39. Fagge LGA
APC: 31,010
PDP: 15,492
40. Kano Munincipal LGA
APC: 65,579
PDP: 15,523
41. Nassarawa LGA
APC: 84,289
PDP: 16,140
42. Tarauni LGA
APC: 52,585
PDP: 7,323
43. Dala LGA
APC: 65,047
PDP: 16,711
44. Rogo LGA
APC: 32,991
PDP: 12,465
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng