Sojojin kasashen yankin Chadi sun fara fadan karshe a yankin da IS ke son mulka

Sojojin kasashen yankin Chadi sun fara fadan karshe a yankin da IS ke son mulka

- MNJTF sun fara sabon tsaro a kogin Chadi don kare miyagun aiyuka yan ta'addan Boko Haram

- Kungiyar hadin kai ce tsakanin rundunoni daga Kamaru, Nijar, Chadi da Najeriya

- Zasu yi amfani da kwarewar su wajen kawo karshen ta'addancin a yankin tafkin na Chadi

Sojojin kasashen yankin Chadi sun fara fadan karshe a yankin da IS ke son mulka
Sojojin kasashen yankin Chadi sun fara fadan karshe a yankin da IS ke son mulka
Asali: UGC

MNJTF sun fara sabon tsaro a kogin Chadi akan aiyukan yan ta'addan Boko Haram daga kusurwar arewaci na kogin Chadi.

Tuni dama an rufe gibin Arege, Metele, Baga da sauran kauyuka na yankin wadanda yan ta'addan suka taba kai hari.

A matsayin matakin kare mutane da dukiyoyin su, MNJTF sun hada da runduna daga Kamaru, Chadi, Jamhuriyar Niger da Najeriya wanda suka sawa rundunar suna operation YANCIN TAFKI.

Amfani aikin shine su mamaye sauran moboyar yan Boko Haram a cikin yankin da suke aikin don tare yan ta'addan.

GA WANNAN: Sakataren PDP na jihar Uzor Kalu ya ajje aikinsa ana tsaka da tsare-tsaren cin zabe

Zamu iya tunawa a watanni kadan da suka gabata, taron shuwagabannin jihohi da hukumar kula da tafkin Chadin, wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta sun yi taron ne a N'Djamena, Chadi don karashe yarjejeniyar da suka fara fara ta shawo kan Boko Haram.

Amfanin wannan aikin shine samar da maslaha don shawo kan matsalar.

MNJTF ta gano kalubale na samar da rahoton hargitsi, ballantana a wannan lokaci na yada labarai marasa tushe ko makama.

Hukumar ta tabbatar da cewa jami'an yada labarai na rundunar zasu maida hankali da kwarewar su don samun cimma manufar su ta kawo karshen ta'addanci a tafkin Chadi tare da kawo daidaito a yankunan da a halin yanzu suka bar gidajen su.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel