Naira zata ruguzo har N415 ga dala $1 muddin aka kara kudiin mai a bana

Naira zata ruguzo har N415 ga dala $1 muddin aka kara kudiin mai a bana

- Masana sun hango wa Najeriya jafa'i

- Wai Naira zata adi warwas kan dala a bana

- Naira ta dogara da mai ne a kasuwar duniya

Naira zata ruguzo har N415 ga dala $1 muddin aka kara kudiin mai a bana
Naira zata ruguzo har N415 ga dala $1 muddin aka kara kudiin mai a bana
Asali: UGC

Wani mummunan labari da muke samu daga sabon rahoton PwC, mai taken ‘Nigeria Economic Outlook Top 10 themes for 2019’ ya hango cewa Nairar Najeriya zata fadi a bana daga N315-N355 da ake samunta yanzu kan kowacce dala, zuwa N390-N415 ga dala.

Wannan na zuwa ne yayin da kasar ke shirin shiga zabe a makon nan, wanda zai iya kawo sabuwar gwamnati mai warwasa kudi ko kuma tazarce ga wannan mai cancana su.

Nairas dai, ta riga ta ta'allaka ne da dala, da kuma farashin mai a kasuwannin duniya. Don haka ne ma ta fadi warwas a 2015-2016, saboda man yayi araha sosai.

GA WANNAN: INEC ta saki nata matsayin kan masu wawason kayan zabe, sai dai ba yadda Buhari yace ba

A cewarsu dai, farashin man fetur a duniya zai iya haddasa raguwar dan kudin da muka tattala a asusun kasashen waje, wanda yanzu ke kan $40b, wanda kuma dashi kasashen duniya ke auna ko kasa na da karin ajiya ko sata.

A cewarsu kuma, akwai yiwuwar gwamnatin tsakiya ta sake cire tallafin man fetur, daga N145 ya hau kamar yadda tayi a baya don tsimi da tanadi, wanda kuma hakan zai harba tsadar rayuwa sama, musamman ga yawa-yawan talakawa.

A dan tsakanin nan kuma, sun hanga suka ce yawan 'yan Najeriya sai kai 210m a 2020, wanda kuwa yawansu talakawane ake haifa ba'a basu isasshen ilimi, agajin da gwamnati ke bayar wa kuma, yana kara yi mata nauyi.

A cewar binciken dai, sai an zubo jari sosai wanda ya kai 26% na GDP dinmu, sannan ne kasar zata sake samun habakar tattalin arzikin 7% kamar yadda ake yawan gani a baya.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel