Gargadin karshe da APC ta yiwa Turawan Yamma: Kuji da matsalolinku na tattalin arziki

Gargadin karshe da APC ta yiwa Turawan Yamma: Kuji da matsalolinku na tattalin arziki

- Jam'iyyar APC ta kara jan kunnen kasashen yammacin duniya akan shishigi ga lamurran kasar nan a karo na biyu

- Najeriya kasa ce mai yanci, don haka bai kamata su dinga shishigi da gatsali akan lamurranta ba

- Dama sun maida hankali akan abubuwa masu muhimmanci da suka shafe su, a nan bazasu bata lokacin su da karfin su ba

Gargadin karshe da APC ta yiwa Turawan Yamma: Kuji da matsalolinku na tattalin arziki

Gargadin karshe da APC ta yiwa Turawan Yamma: Kuji da matsalolinku na tattalin arziki
Source: Facebook

Jam'iyyar APC ta kara wanke kasashen yammacin duniya akan zargin da take musu na cewa suna tsoma kansu akan zabe na Najeriya.

Mataimakin sakataren yada labarai na jam'iyyar mai mulki, Yekini Nabena, a ranar litinin a Abuja yace kasashen yammacin zai fi idan suka maida hankali kan kalubalen dake ci musu tuwo a kwarya a maimakon maida hankali akan lamurran Najeriya.

Yace: "A duk zabukan da mukeyi a kasar, muna maraba da masu lura na cikin gida da kuma kasashen waje. A tunanin mu wannan al'ada ce mai kyau kuma muna yinta ne don tabbatar da munyi zabe na gaskiya,"

"Amma tsokaci akan zaben mu dake fitowa daga bakunan wasu yan diflomasiyyar yamma da kuma tantattun masu lura na kasashen waje suna nuna gatsali da tsoma kai wanda bai dace ba,"

"Najeriya kasa ce mai yancin zartar da hukuncin kanta da kanta kuma abinda kasashen yammacin keyi bai dace da dokokin mu'amala tsakanin kasa da kasa da kuma shiga yancin kasa mai zaman kanta."

Mai magana da yawun jam'iyyar APC yayi kira ga yan Najeriya dasu shirya kare yancin kasar su a kowanne lokaci.

"Duk da yananyin shirin zabe ba dole ya zamo yanda ake so ba akan daga zaben da akayi ana gab da yin shi, dole ne muyi aiki tare don tabbatar da kasar mu ta gyaru."

GA WANNAN: 'Dage zabe da INEC tayi wani mummunan shiri ne kan mulkin Buhari'

Maganganun yan dilflomasiyya da kuma tantattun masu lura daga kasashen wajen na cire mana yakini adon haka ne muka kushe su. A matsayin mu na kasa, zamu samo hanyar shawo kan matsalolin mu a cikin gida duk lokacin da suka taso. Inji shi.

"US, UK da EU na da isassun matsaloli. Lokacin su da karfin su yakamata su saka don shawo kan zargin da ake ma Rasha na shishigi a zaben US da ya wuce, lalacewar yarjejeniyar Brexit tsakanin UK da EU da sauran manyan matsalolin su."

Da yayi magana akan dage zaben da hukumar zabe mai zaman kanta tayi, ya nuna damuwar shi amma ya roki hukumar zaben da ta toshe duk hanyoyin baraka da ta hango don samu zabe mai kyau, na yanci da kuma nagarta a ranar asabar.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel