Siyasar Kano: Ku kasa, ku tsare, ku raka, ku jira, a zaben 2019 – Kwankwaso

Siyasar Kano: Ku kasa, ku tsare, ku raka, ku jira, a zaben 2019 – Kwankwaso

- Jam’iyyar PDP ta zagaya kowace karamar hukuma tana yawon yakin neman zabe a Kano

- Tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso ya ziyarci Gwale inda ‘Dan takarar PDP ya fito

- Injiniya Kwankwaso yace a 2019 ana sa rai cewa Gwamna ya fito daga cikin Birnin Kano

- Sanatan jihar ya fadawa Jama'a su tafi ofishin INEC su tsare kuri'ar su bayan sun yi zabe

Siyasar Kano: Ku kasa, ku tsare, ku raka, ku jira a zaben 2019 – Kwankwaso
Kwankwaso ya tuna da Marigayi Sheikh Jafar wajen taron PDP
Asali: Facebook

A jiya ne tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, da jirgin yakin jam’iyyar PDP su ka gama zagaye kaf kananan hukumomin Kano domin ganin an samu nasara a zaben 2019 da za ayi cikin ‘yan kwanakin nan.

Sanata Rabiu Kwankwaso ya shiga karamar hukumar Gwale inda yayi kira ga Mutanen yankin su tabbata sun ga jam’iyyar adawa ta samu nasara a zaben da za ayi inda PDP ta ke sa rai cewa gwamna zai fito daga Gwale.

KU KARANTA: Ba na shakkar mu buga da Rabiu Kwankwaso – Shekarau

Tsohon gwamnan ya kuma fadawa Matasa su shirya tsare kuri’un su a zaben da za ayi tare da kuma gujewa siyasar daba. Kwankwaso yake cewa yanzu lokaci yayi da za a samu gwamna daga cikin birnin Kano a wannan karo.

A wajen taron, tsohon gwamnan ya kuma yi addu’a ga Marigayi Malam Jafar Mahmud Adam wanda aka kashe a 2007. Injiniya Kwankwaso ya bayyana cewa har gobe yana sa rai za a gano wanda su ka kashe wannan babban Malamin.

Rabiu Kwankwaso ya yabawa wannan Shehin Malami wanda asalin sa Mutumin Daura ne da aka yi wa kisan gilla a Kano inda yace Mutumin kwarai ne na Allah. Hakan na zuwa ne bayan an ji Sanatan yana sukar wasu Malaman jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel