Ka tona manyan barayin da suke wurinka neman mafaka in kai mai gaskiya ne - gwamnan PDP ga Baba

Ka tona manyan barayin da suke wurinka neman mafaka in kai mai gaskiya ne - gwamnan PDP ga Baba

- Gwamna Emmanuel na jihar Akwa Ibom ya kalubalanci Buhari da gwamnatin shi akan su fito da masu cin rashawa dake boyewa karkashin su

- Gwamnan yace sun kammala shirin tura mutane 1000 akan kowanne akwati gudun magudin zabe daga APC

- Ya jinjinawa kananan hukumomi 30 na jihar sakamakon goyon bayan da suka nuna mishi yayin kamfen

Ka tona manyan barayin da suke wurinka neman mafaka in kai mai gaskiya ne - gwamnan PDP ga Baba
Ka tona manyan barayin da suke wurinka neman mafaka in kai mai gaskiya ne - gwamnan PDP ga Baba
Asali: Depositphotos

Gwamnan jihar Akwa Ibom, Mr Udom Emmanuel ya kalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma gwamnatin tarayya dasu hukunta duk wani dan siyasa da aka kama da laifin rashawa kuma ya tsere APC don gudun shari'a ta hau kan shi.

Emmanuel wanda ya sanar da hakan a yayin kammala kamfen din neman komawa kujerar shi a karamar hukumar Onna, yace ya kalubalanci shugaban kasa da gwamnatin shi wadanda suke ikirarin suna yaki da rashawa.

Yace shugaban ya yankewa mahandaman hukunci da kuma wadanda ke wawushe haraji daga baya su tsere zuwa APC don adana abinda suka wawura.

"Ba dole yan Najeriya su san wannan ba. Idan kaga muagayen mutanen na fitowa don fadin duk abinda sukayi niyya, kasan cewa duk abinda suke ikirari gwamnatin nan ce ta goyi bayan su,"

"Zancen wawure haraji ko? Shiyasa suke gudu can su boye. Amma ina kalubalantar gwamnatin tarayya tunda tace tana fada da rashawa, toh su fara bayyana wadanda ke boyewa a bayan su. Su fito dasu don bayyana mana amsar yanda haraji ya gudu. Su amsa mana komai," inji gwamnan.

GA WANNAN: EFCC ta sake chafko matasa masu zambo cikin aminci su 11

Ya bayyana cewa PDP ta kammala tsarin ta na tura mutane 1,000 a kowanne akwatin zabe na ang ranakun asabar 16 ga watan fabrairu da 2 ga watan maris, don kare mazabu da kuma tarwatsa shirin yan adawa na kin yin zabe mai kyau da nagarta cike da zaman lafiya da yanci a jihar.

Emmanuel yace jam'iyyar APC a jihar tayi duk yanda zatayi don sa guiwar mutane ta saki a jihar amma har yanzu basu yi nasara ba. Ya jinjinawa matasan PDPn da suka rungumi zaman lafiya a gwamnatin tashi ta hanyar nuna hakan har a lokutan kamfen duk da anso harzuka su.

Emmanuel yace hakan ya kara fusata jam'iyyar adawa don tayi hakan ne da zummar ta kama wasu jiga jigan yan PDPn ta tsare su har sai bayan zabe.

Gwamnan yayi godiya ga duk kananan hukumomi 30 a Akwa Ibom da ya ziyarta sakamakon tsayuwar su tsayin daka akan kamfen din jam'iyyar shi.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel