Wannan zabe da zamu shiga, dama ce ta qara danqon zumunta ga al'ummun Najeriya - Buhari

Wannan zabe da zamu shiga, dama ce ta qara danqon zumunta ga al'ummun Najeriya - Buhari

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hori yan Najeriya da su dubi zabe a matsayin hanyar karfafa hadin kan kasa

- Ya roki matasa da su watsar da duk wani nau'i na hargitsi da hayaniya lokacin zabe

- Atiku yayi kira da shugaba Buhari da yayi amfani da ofishin shi wajen ganin duk wanda yasa kuri'a tayi amfani

Wannan zabe da zamu shiga, dama ce ta qara danqon zumunta ga al'ummun Najeriya - Buhari

Wannan zabe da zamu shiga, dama ce ta qara danqon zumunta ga al'ummun Najeriya - Buhari
Source: UGC

A ranar laraba, shugaban kasa Muhammadu Buhari, a Abuja ya shawarci yan Najeriya dasu dubi zabe mai zuwa a matsayin damar karfafa hadin kan kasar nan.

Buhari ya bada shawarar a jawabin da yayi jim kadan bayan sa hannu da yayi a yarjejeniyar zaman lafiya da sauran yan takarar kujerar shugaban kasa wanda ya hada da Abubakar Atiku na jam'iyyar adawa ta PDP.

Yayin kira ga yan Najeriya akan su fito kwan su da kwarkwata wajen kada kuri'a, Buhari ya shawarci duk masu ruwa da tsaki dasu saka bukatar kasa ta zama farko kafin bukatun su.

"Zabubbukan suna da amfani saboda suna kawo zaman lafiya da cigaban kasa. Ina mika bukata ta ta musamman ga matasa da kada su bari ayi amfani dasu wajen hargitsin zabe.

"Ina rokon ku daku watsar da duk wani nau'in hargitsi su kuma hada. Zamu zabi jam'iyyu amma a karshe jam'iyyar da tayi nasar ce jam'iyyar Najeriya, kasar mu. Zabukan na da amfani amma don su kara mana karfi. Muyi iya kokarin mu kuma mu roki ubangiji," inji shi.

Wannan zabe da zamu shiga, dama ce ta qara danqon zumunta ga al'ummun Najeriya - Buhari

Wannan zabe da zamu shiga, dama ce ta qara danqon zumunta ga al'ummun Najeriya - Buhari
Source: UGC

Buhari, wanda shine dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC, yace hukumar zabe mai zaman kanta ta shirya tsaf don tabbatar da zabe mai kyau.

Yace an wayar ma da jami'an tsaro kai akan aiyukan su don tabbatar da nasarar zaben.

Atiku ya hori shugabanni da jami'an hukumar zabe, yan sanda da sauran jami'an tsaro da su yi gaskiya a zabe mai zuwa.Ya hori jami'an tsaro dasu yi gaskiya ta hanyar kama wadanda ya dace ba wai yan adawa ba kafin zabe.

"Akwai yuwuwar damokaradiyyar mu ta kara karfi a zaben 2019 fiye da 2015, wanda akayi shi cikin yanci da gaskiya har jam'iyyar adawa ta hau mulki,"

"Ina rokon shugaba Buhari da yayi amfani da ofishin shi don tabbatar da cewa duk wanda ya cancanta yayi zabe yayi kuma Kuri'ar tayi amfani," inji shi.

GA WANNAN: An yaba wa hukumar zabe ya INEC kan tunawa da nakasassu masu jefa quri’a

Atiku ya tunatar da sauran yan takarar cewa zabe anayin shi ne don kasa kuma dole ne abi zabin yan Najeriya.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel