EFCC tayi ram da Jamila Shu'aibu da abokan damfararta a Abuja

EFCC tayi ram da Jamila Shu'aibu da abokan damfararta a Abuja

- Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta cafke wasu mutane 10

- Wadannan mutane sunayin damfara ne ta hanyar yanar gizo

-An samu nasarar kama su a ranar 7 ga watan Fabrairu

EFCC tayi ram da Jamila Shu'aibu da abbokan damfararta a Abuja

EFCC tayi ram da Jamila Shu'aibu da abbokan damfararta a Abuja
Source: Facebook

Hukumar dake yaki dacin hanci da rashawa ta (EFCC) ta samu nasarar kama wasu mutane 10 dake damfara ta hanyar yanar gizo.

Wadanda aka kama din sun hada da Triumph Chikwendu Madumere,Success Chukwumazu Obasi, Jamila Shuaibu, Bright Idumwonyi Osaigboko da kuma Obasi Wisdom.

EFCC tayi ram da Jamila Shu'aibu da abbokan damfararta a Abuja

EFCC tayi ram da Jamila Shu'aibu da abbokan damfararta a Abuja
Source: Facebook

Ragowar sun hada da Idemudia Emmanuel, Sandra Alang,Stanley Ohiaeri,Samuel Tochukwu da kuma Ikechukwu David Ohiaeri.

GA WANNAN: Buhari ko Atiku daya daga cikinsu ne zai kafa gwamna a jihar Filato

An samu nasarar kama su a Karu da Mpape dake Abuja a ranar 7 ga watan Fabrairu shekara ta 2019.

EFCC tayi ram da Jamila Shu'aibu da abbokan damfararta a Abuja

EFCC tayi ram da Jamila Shu'aibu da abbokan damfararta a Abuja
Source: Facebook

A lokacin da aka kamasu an samesu da mota guda Uku kirar Mercedes Benz, laptop Biyar, wayoyin hannu 10, da katin jirar kudi na banki (ATM).

Nan bada jimawa ba za'a gurfanar dasu a gaban kotu.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel