Takarar shugaban kasa: Nine zabin Shehu Yar'Adua tun 1993 - Atiku

Takarar shugaban kasa: Nine zabin Shehu Yar'Adua tun 1993 - Atiku

- Dan takarar shugabancin kasa na PDP, Atiku Abubakar ya fadawa Katsinawa cewa marigayi Shehu Yar'Adua ya zabe shi a matsayin shugabancin Najeriya tun 1993

- Atiku Abubakar ya roki Katsinawa su taimaka masa domin ganin wannan mafarkin na marigayi Yar'Adua ta zama gaskiya

- Ya yi alkawarin kawar da yunwa da fatara daga Najeriya tare da dawo da martabar kasar a idanun kasashen duniya idan an zabe shi

A ranar Alhamis ne dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP a zaben ranar 16 ga watan Fabrairu, Atiku Abubakar ya ce marigayi Janar Shehu Musa Yar'Adua ya zabi shi domin zaman shugaban kasar Najeriya tun a 1993.

Takarar shugaban kasa: Nine zabin Shehu Yar'Adua tun 1993 - Atiku

Takarar shugaban kasa: Nine zabin Shehu Yar'Adua tun 1993 - Atiku
Source: UGC

DUBA WANNAN: Hotunan yadda kaddamar da yakin neman zaben Buhari ta kasance a Adamawa

Atiku ya yi wannan ikirarin ne a yayin da ya ke jawabi da taron jiga-jigai da magoya bayansa a yayin kaddamar da yakin neman zabensa a Karakanda Stadium da ke jihar Katsina.

A jawabin da dan takarar shugaban kasar ya yi cikin harshen hausa, ya ce, "Marigayi Shehu Yar'Adua ya zabe ni a matsayin shugaban kasar Najeriya tun a 1993. Yanayin siyasar Najeriya ce ta hana hakan afkuwa.

"Ina kira a gare ku Katsinawa ku tallafa min domin ganin mafarkin Yar'Adua ya zama gaskiya. Ku zabe n domin in kawar da yunwa da fatara daga Najeriya. Ku zabi Yaku Lado a matsayin gwamna domin jihar mu ta Katsina da samun cigaban da gwamnatin APC ta gaza samarwa."

Tsohon gwamnan jihar Katsina, Shehu Shema da ya yi jawabi a wurin taron shima ya yi kira ga masu zabe su kada kuri'arsu ga 'yan takarar jam'iyyar PDP.

Ya ce, "Alhaji Atiku Abubakar shine mutumin da zai iya mulkin Najeriya a yanzu. Lokaci ya yi da zamu zabi mutumin da ke kwarewa ya kuma hada kan Najeriya. Atiku shine wanda zai iya gudanar da wannan aikin.

"Idan kuka zabe shi a matsayin shugaban kasa, zai kawar da yunwa da fatara daga Najeriya, zai kuma tabbatar Najeriya ta dawo da mutunci da martabar ta idanun kasashen duniya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel