Dalilin da ya sa mu ka janye yajin aiki – ASUU

Dalilin da ya sa mu ka janye yajin aiki – ASUU

- A yau ne kungiyar malaman jami’o’I ta sanar da janye yajin aikin da ta dauki tsawon watanni uku ta na yi

- Shugaban kungiyar, Farfesa Biodun Ogunyemi, ne ya sanar da janye yajin aikin yayin wata ganawa da manema labarai a Abuja

- ASUU ta shiga yajin aiki ne tun watan Nuwamba na shekarar 2018 bayan ta zargi gwamnati da nuna halin ko-in-kula a kan bangaren ilimi

A yau, Alhamis, ne kungiyar malaman jami’o’I ta sanar da janye yajin aikin da ta dauki tsawon watanni uku ta na yi.

Shugaban kungiyar na kasa, Farfesa Biodun Ogunyemi, ne ya sanar da janye yajin aikin yayin wata ganawa da manema labarai a Abuja, birnin tarayya.

Kungiyar ta janye yajin aikin ne bayan wata gana wa da wakilan gwamnatin tarayya da ministan kwadago da samar da aiyuka, Sanata Chris Ngige, ya jagoranta.

ASUU ta ce ta janye yajin aikin ne bayan kamala tuntuba da tattauna wa a kan tayin da gwamnatin ta yi a kan bukatun da kungiyar ta bukaci a cika ma ta kafin ta koma bakin aiki.

Dalilin da ya sa mu ka janye yajin aiki – ASUU
Tattaunawar ASUU da gwamnatin tarayya
Asali: UGC

A sanarwar da ta fitar, ASU ta ce bayan amince wa da gwmnatin tarayya ta yi na sakin biliyan N20 domin biyan malaman jami’o’I bashin alawus da su ke bi a shekarar 2018, gwamnatin ta yi alkawarin sake fitar da wata biliyan N25bn a watan Afrilu zuwa Mayu na shekarar nan, bayan haka kuma gwamnatin za ta cigaba da zartar da yarjejeniyar da su ka kulla da ASUU tun shekarar 2013.

DUBA WANNAN: Zabe: Ba mu da dan takara a Najeriya – Gwamnatin Amurka

ASUU ta yi godiya ga kungiyoyi daban-daban, musamman kungiyar kwadago, bias goyon baya da hadin kan da su k aba su yayin yajin aikin.

Kazalika, kungiyar ta ASUU ta yi Alla-wadai da halayyar wasu shugabannin jami’o’in kasar bias yunkurin yin kafar angulu ga yajin aikin.

ASUU ta shiga yajin aiki ne tun watan Nuwamba na shekarar 2018 bayan ta zargi gwamnati da nuna halin ko-in-kula a kan bangaren ilimi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng